Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar ministocinsa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari jagoranci zaman majalisar zartarwa da aka yi a ranar Laraba 24 ga watan Oktoba a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda aka saba kowanne wata.
Majiyar LEGIT.com ta ruwaito an fara taronne da misalin karfe 11 na safe, daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa dakin taron, yayin da mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo ya isa mintuna biyar kafin isar shugaba Buhari.
KU KARANTA: Zagi da aibanta jami’in Dansandan Najeriya ya jefa wata mata cikin tsaka mai wuya
Rahoton ya kara da bayyana cewa zaman majalisar na yau ya yi armashi saboda halartar kusan kafatanin Ministocin da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya, ba kamar yadda suke kin zuwa ba idan har mataimakin shugaba Osibanjo ne yake jagoranta.
Daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka halarci taron zaman akwai Sakataren gwamnati, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan tarayya, Winifred Ita-Eyo, mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro, Babagana Munguno da sai sauransu.
Da farin taron, shugaba Buhari ya umarc Ministan ayyuka, gidaje da lantarki, Babatunde Fashola daya gabatar da addu’ar musulunci kafin a fara zaman, yayin da ya umarci Ministan kwadago, Sanata Ngige ya gabatar da addu’ar Kiristoci.
Daga cikin ministocin da suka halarci zaman akwai ministan Abuja, Muhammed Bello, na watsa labar Lai Muhammad, na kudi Zainab Shamsuna, na sadarwa Adebayo Shittu, na Neja Dealta Uguru Usani, na cikin gida Abdul Rahman Dambazau.
Sauran sun hada da Ministan Ilimi Adamu Adamu, ministan sharia Abubakar Malami, ministan kiwon lafiya Isaac Adewole, ministan kasafin kudi da tsare tsare Udo Udoma da minister noma Audu Ogbeh.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng