Majalisar dokoki ta amince da sabbin kwamishinoni 21 a Borno

Majalisar dokoki ta amince da sabbin kwamishinoni 21 a Borno

Majalisar dokokin jahar Borno ta sanar da amincewa da sunayen mutane 21 da gwamnan jahar, Kashim Shettima ya aika mata wadanda yake so su maye gurbin tsofaffin kwamishinonin daya sallama daga aiki, domin su tantancesu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kaakakin majalisar, Abdulkarim Lawan ne ya bayyana haka a ranar Talata 23 ga watan Oktoba, a yayin da yake karanto sunayen kwamishinonin da suka kamala tantancewa tare da amincewa dasu.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: Omoyele Sowore ya zabo mataimakinsa daga jahar Jigawa

Sai dai majiyarmu ta ruwaito daga cikin sunaye 21 da majalisar ta amince dasu, akwai adadin sunaye goma daga cikin tsofaffin kwamishinonin da aka rusa, da kuma sabbin sunaye guda goma sha daya.

Majalisar dokoki ta amince da sabbin kwamishinoni 21 a Borno
Kashim
Asali: Facebook

Idan za’a tuna a ranar Talata 28 ga watan Satumba ne Kashim Shettima ya sanar da rushe kafatanin majalisar zartarwar jahar Borno, karo na farko tun bayan lashe zabensa na gwamnan jahar a shekarar 2015.

Sakataren gwamnatin jahar, Usman Shuwa ne ya sanar da haka, inda yace kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa gwamna damar tsige kwamishinoninsa, sa’annan gwamnan yana yi ma tsofaffin kwamishinonin fatan alheri.

A wani labarin kuma, shirye shirye sun yi nisa a jam’iyyar APC na shirye shiryen ganin dan takararta na mukamin gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai labara a zaben shekarar 2019.

Babagana Zulum wandake rike da mukamin kwamishinan sake farfado da yankunan da ayyukan ta’addanci ya shafa ya samu nasara a zaben fidda yan takara ne daya gudana a filin kwallon El-Kanemi Warriors.

Wasu masana siyasar jahar Borno sun tabbatar da nasarar da Zulum ya samu baya rasa nasaba da goyon bayan da gwamnan jahar,Kashim Shettima ya bashi, hakan yasa ya samu kuri’u 4, 432 cikin kuriu 4,571 da aka kada.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng