Ishaq Hadejia ya bukaci Minista Suleiman Adamu ya yi murabus

Ishaq Hadejia ya bukaci Minista Suleiman Adamu ya yi murabus

- Wani jigo a jam'iyyar APC a Jihar Jigawa, Ishaq Hadejia ya yi ikirarin cewar Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu ya yi watsi da jihar

- Hadejia ya yi ikiraron cewar Adamu baya tallafawa al'ummar jihar duk lokcin da wani iftila'i ya fada musu

- Jigon na APC ya yi ikirarin cewar Ministan na Ruwa ya ki bawa Hukumar Ayyukan Gona hadin kai domin habbaka noma a jihar

Wani jigo a jam'iyyar All Progress Party (APC) a Jihar Jigawa, Ishaq Hadejia ya yi kia da Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu ya yi murabus daga mukaminsa nan take.

Hadejia ya yi wannan maganar ne a yayin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a Dutse a ranar Litinin 22 ga watan Oktoba.

Jigo a jam'iyyar APC ya nemi ministan Buhari ya yi murabus
Jigo a jam'iyyar APC ya nemi ministan Buhari ya yi murabus
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Masoyin Atiku da ya tuka keke daga Owerri zuwa Abuja ya kare a gadon asibiti

Ya yi ikirarin cewar Adamu baya hallartan taron siyasa da wasu sauran harkoki a jihar inda ya ce dama shi ba dan siyasa ba ne.

Hadejia ya yi korafi kan yadda duk lokacin da wani abu ya faru da al'ummar jihar na farin ciki ko akasin haka, Ministan ba ya taba zuwa jihar domin taya su muran ko kuma yin jaje.

"Ambaliyar ruwa da ta faru a jihar Jigawa kwana-kwanan nan ya shafi unguwani 500 a jihar, tare da rasa rayyuka 40 da asarar kayan abinci, gonaki, dabobi da dukiyoyi amma ministan bai zo ya yiwa al'ummarsa jaje ba," inji shi.

Ya kuma ce akwai manoma da yawa a Jihar Jigawa amma a matsayinsa na Ministan Albarkatun Ruwa bai taba yin hadin gwiwa da Hukumar Aikin Noma ba domin kawo cigaba a Jihar Jigawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel