Fusatattun 'yan takara 300 sun dunguma sun fita daga APC a Kano

Fusatattun 'yan takara 300 sun dunguma sun fita daga APC a Kano

A kalla 'yan takara 300 ne da su ka nemi APC ta tsayar da su takara a kujeru daban-daban su ka dunguma su ka fice daga jam'iyyar a yau, Litinin.

'Yan takarar sun byyana cewar tsagwaron rashin adalcin da aka nuna ma su a APC ne ya tunzura su ka bar jam'iyyar.

Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kammala wani taro a gidansa, kakakin fusatattun 'yan takarar, Sanata Isa Yahaya Zarewa, ya bayyana cewar sun fit daga jam'iyyar APC daga yau.

"A kowacce tafiyar siyasa da ta ke bukatar dorewa dole a bawa dimokradiyyar cikin jam'iyya muhimmanci.

"Daga abun da ya faru a zaben fidda 'yan takarar a APC, ta tabbata cewar babu maganar dimokradiyya a cikin jam'iyyar," a cewar Zarewa.

Sannan ya cigaba da cewa, "An yi mana ba daidai ba amma duk da haka shugabancin jiha da na kasa bai saurari kokenmu ba balle a bamu hakuri. Hakan ya nuna cewar ba mu da wani muhimmanci a wurin jam'iyyar APC duk kasancewar mu na cikin ma su ruwa da tsaki da su ka gina jam'iyyar.

Zarewa ya bayyana cewar ficewar 'yan takara a kalla 300 daga APC barazana ce ga nasarar jam'iyyar a zaben shekarar 2019.

Kazalika, ya bayyana cewar ya zuwa yanzu ba su yanke shawarar jam'iyyar da za su shiga ba amma su na ma su sanar da jama'a cewar sun fita daga APC.

Daga karhe ya yi kira ga magoyya bayansu da su bi sahun su, su fita daga APC tare da yin albishir din cewar kwanan nan wadanda su ka kore su daga jam'iyyar za su yi nadama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel