Ali Nuhu ya nada Nafisa Abdullahi a matsayin uwargidan kamfaninsa

Ali Nuhu ya nada Nafisa Abdullahi a matsayin uwargidan kamfaninsa

Shahararren Jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sarki Ali Nuhu, ya nada fitacciyar jaruma, Nafisa Abdullahi, a matsayin uwargidan kamfaninsa na shirin fim.

A wani sako da ya saki a shafinsa na dandalin sada zumunta (Instagram), Ali Nuhu, ya bayyana cewar ya nada jarumar a mukamin ne saboda kwarewar ta a cikin shirin fim.

"Ma'anar uwargida shine wata mace da ta zama daban. Ta fara shirin fim tun daga kasa har ta samu daukaka zuwa fitacciyar jaruma da ta lashe kyauta masana'antar Kannywood. Ta zama jaruma saboda gogewar da take da ita a harkar fim. Ina mai gabatar ma ku da Nafisa Abdullahi a matsayin uwargidan kamfanin shirya fina-finai na FKD," kamar yadda Ali Nuhu ya rubuta.

Kamfanin shirya fina-finai na FKD ya dade yana fitar da fina-finai da da su ka yi fice masana'antar Kannywood.

Ali Nuhu ya nada Nafisa Abdullahi a matsayin uwargidan kamfaninsa
Ali Nuhu da Nafisa Abdullahi
Asali: Twitter

Ko a kwanakin baya, jaridar Legit.ng kawo ma ku labarin cewar fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya samu kayautar digirin girmamawa a kan koyar da sana'a da cigaban matasa daga jami'ar ISM Adonai ta kasar Amurka dake da matsuguni a garin Kotono na kasar Benin.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin jaruman fina-finan Hausa maza da mata, hotuna

Jami'ar ta karrama Ali Nuhu ne yayin wani bikin yaye dalibai da bayar da digirin girmamawa na zangon karatu na 2017/2018 da aka gudanar a birnin Lome na kasar Togo a ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoba.

Yayin bikin, magatakardar jami'ar, Adamu Muhammad, ya bayyana cewar aiyukan taimako da tallafawa da Ali Nuhu ke yi ne ya dauki hankalin jami'ar har ta yanke shawarar karrama shi. A nasa jawabin, Ali Nuhu, ya godewa mahukuntar jami'ar da karramawar da suka yi masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel