Dan takarar Sanata a APC ya maka jam'iyya a kotu bisa canja sunansa
- Wani dan takarar Sanata a jihar Niger ya shigar da kara kotu saboda uwar jam'iyyar APC ta cire sunansa cikin jerin sunayen da ta kaima INEC
- Jam'iyyar APC ta maye gurbin Sani Musa ne da Sanata mai ci a yanzu, Sanata David Umaru mai wakiltan Niger ta Gabas
- Sani ya yi korafin cewar dama uwar jam'iyyar a bukaci su janyewa sanatoci masu ci amma suka ki amincewa da hakan saboda ba su ne suka lashe zaben cikin gida ba
Alhaji Sani Musa (313) wanda shine ya lashe tikitin takarar Sanata na yankin Niger ta Gabas karkashin jam'iyyar APC ya garzaya kotu domin kalubalantar yadda uwar jam'iyyar wadda ta maye gurbin sunansa da Sanata mai ci yanzu na mazabar, Sanata David Umaru.
Sunan Sanata Umaru yana cikin jerin sunayen 'yan takarar da jam'iyyar ta APC ta mika ga Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC a jiya Alhamis.
DUBA WANNAN: APC tayi burus da umurnin INEC, ta mika sunayen 'yan takarar jihar Zamfara
"Mun tuntubi lauyoyinmu, za mu tafi kotu domin kallubalantar wannan rashin adalcin da a kayi mana," inji Alhaji Nma Kolo, daya daga cikin mamban kwamitin masu bawa Sani Musa shawara.
Kolo ya kara cewa: "Ciyaman din jam'iyyar na kasa ya bayyana cewar yana son dukkan sanatocin da ke kan mulki su koma majalisar ba tare da hammaya ba amma muka ki amincewa da hakan saboda anyi zabe kuma an samu wadanda su kayi nasara.
"Munyi mamakin ganin cewar uwar jam'iyyar ta doge kan bakanta na ganin cewar dole sai tsaffin Sanatocin sun koma majalisar."
Kolo ya yi kira ga al'ummar mazabar su kwantar da hankullansu kuma kada su dauki doka a hannunsu inda ya tabbatar da cewar za suyi duk mai yiwuwa domin ganin basu hakkinsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng