Fiye da malaman firamari 5000 sun samu horo akan dabarun koyarwa a Kaduna
Gwamnatin jahar Kaduna ta shirya horaswa na musamman ga malaman fimari su duu biyar da dari takwas da talatin da hudu (5,834) akan hanyoyin da zasu inganta rubutu da karatun dalibansu na Firamari, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeiriya, NAN.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito shugaban cibiyar hadin kai na ilimI, GPE, Hajiya Haliman Jumare ce ta bayyana haka a ranar Laraba a garin Kaduna, inda tace an horar da malaman ne akan hanyoyin da zasu janyo hakulan dalibansu ta hanyar rawa da wake wake.
KU KARANTA: Zaben shugaban kasa: Bamu da yar mowa ko yar bora a Najeriya – Amurka
Jumare tace binciken masan ya nuna wannan hanyar ita ce hanyar da tafi inganci wajen koyar da yara rubuta da karatu, ta kara da cewa malamai dubu daya da casa’in da biyu ne suka samu horon a watan satumba, yayin da wasu dubu hudu da dari bakwai da arba’in da biyu ke samun horon a yanzu haka.
“Cikin aikin hadin gwiwa da cibiyar Universal Learning Solutions, ULS, mun horas da malamai 1,000 da jami’a 92, tare da tallafi daga hukumar ilimi ta bai daya a watan Satumba. fahimtar muhimmancin wannan tsarin koyarwar ne ya sanya gwamnatin jahar ta samar ma malamai wannan horo.
“Kwamishinan ilimi na jahar, Malam Jafaru Sani ya amince da Karin sabbin Malamai 3,000, shuwagabannin makarantu 1,500 da jami’ai 242 da zasu samu wannan horo, da wannan ne adadin wadanda muka horas a cikin watanni biyu zuwa 5,834.” Inji ta.
Daga karshe Hajiya Jumare ta yi kira ga malaman da suka samu horon akan cewa ya kamata a ga canji a tsare tsaren koyarwarsu musamman bayan sun samun wannan horo, saboda gwamnati ta kashe makudan kudade wajen shirya taron.
Guda daga cikin malaman da suka amfana da wannan horo, Hauwa Sherika ta yaba da kokarin gwamnatin jahar data kirkiro da wannan horo, inda tace an koya musu dabarun koyar da yara cikin kwanciyar hankali da nishadi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng