Sunaye: Kwamishinoni 4, AIG 3 da hukumar 'yan sanda ta karawa girma

Sunaye: Kwamishinoni 4, AIG 3 da hukumar 'yan sanda ta karawa girma

A yau, Laraba, ne Hukumar kula da 'yan sandan Najeriya (PSC) ta amince da karawa wasu Kwamishinoni 4 da mataimakan Sifeton 'yan sanda 3 girma.

An karawa Kwamishinonin 4 girma ne zuwa mukamin mataimakan babban Sifeton 'yan sanda(AIG), yayin da aka karawa mataimakan Sifeton 3 girma zuwa mataimaka masu daraja ta daya(DIG), kamar yadda sanarwar da Ikechukwu Ani, jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda, ya sanar a Abuja.

Sabbin mataimakan babban Sifeton da aka daga darajar su akwai Musa Muhammed, wanda shine ke rike da makarantar horar da manyan jami'an 'yan sanda da ke Kuru a Jos; Mohammed Usman, kwamandan makarantar horon 'yan sanda da ke Wudil a jihar Kano; da Peace Ibekwe Abdallah, jami'in hukumar 'yan sanda a ofishin mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro.

Sunaye: Kwamishinoni 4, AIG 3 da hukumar 'yan sanda ta karawa girma
Jami'an 'yan sanda
Asali: Facebook

Kwamishinonin da aka yiwa karin girma su ne: Godwin Nwobodo, kwamishinan 'yan sanda mai kula da tsara kwasa-kwasai makarantar horon 'yan sanda ta Wudil; Adeyemi Samuel, kwamishinan 'yan sanda a jihar Akwa Ibom; Augustine Iornongu Iwar, kwamishinan 'yan sanda a jihar Bayelsa; da Adekunle Oladunjoye, kwamishina mai kula da tsare-tsare a shelkwatar 'yan sanda ta kasa da ke Abuja.

DUBA WANNAN: Dakarun soji sun ceto mata 7 da yara 5 daga hannun 'yan Boko Haram, hotuna

Shugaban hukumar PSC, Musliu Smith, ya bukaci jami'an da aka karawa girman su kara zage dantse domin hidimtawa kasa kamar yadda su ka saba.

Kazalika, ya bayyana cewar tuni hukumar ta a aike da sunayen jami'an ga Sifeton rundunar 'yan sanda, Ibrahim Idris, domin tabbatar da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng