Wani Matashi ya yi garkuwa da Mahaifiyar Budurwar sa a jihar Abia

Wani Matashi ya yi garkuwa da Mahaifiyar Budurwar sa a jihar Abia

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wani Matashi, Chinindu Innocent, ya shiga hannun hukumar 'yan sanda da laifin garkuwa da Mahaifiyar Budurwar sa a karamar hukumar Ukwa ta jihar Abia dake Kudancin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, Chinindu tare da wasu abokanan su uku; Ekendu Chidiebere, Tochukwu Samuel da kuma Ikechukwu Nwankwo, sun shiga hannun hukumar 'yan sanda da suka tarayya wajen aikata wannan mummunan laifi.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, hukumar 'yan sandan bisa jagorancin mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari, ta samu nasarar cafke wannan miyagun mutane kwanaki kadan bayan sun karbe N300, 000 na kudin fansar garkuwar da suka yi.

Wani Matashi ya yi garkuwa da Mahaifiyar Budurwar sa a jihar Abia
Wani Matashi ya yi garkuwa da Mahaifiyar Budurwar sa a jihar Abia
Asali: UGC

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, Chinindu mai shekaru 24 a duniya ya kull kitimurmurar garkuwa da Mahaifiyar Budurwar sa inda ya kunshe ta cikin wani dakii a yankin Ogwu dake jihar ta Abia.

KARANTA KUMA: Gwamna Masari da Okorocha sun shiga bayan Labule da Shugaba Buhari

A yayin da Chinindu ya sha titsiye na hukumar 'yan sanda, ya amsa laifin sa cikin gaggawa da cewar ya aikata hakan ne domin ya kuntatawa Budurwarsa da ta nemi rabuwa da shi da har ta kulla sabuwar alaka ta soyayya da wanin sa.

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, an tsare wannan Matasa 4 a babban ofishin 'yan sanda na kasar nan dake garin Abuja domin ci gaba da gudanar da bincike na diddigi akan lamarin.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel