Abin da ya sa Shugaba Buhari bai isa ya hana ni barin Najeriya ba - Bafarawa
- Attahiru Bafarawa ya nemi a cire sunan sa daga cikin wadanda aka hana barin Najeriya
- Tsohon Gwamnan na Sokoto yace Kotu ta bincike sa kuma ba a same sa da wani laifi ba
- ‘Dan takaran na Shugaban kasa a PDP yace yanzu haka sam babu inda ake binciken sa
Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya nemi ayi maza a cire sunan sa daga wadanda aka haramtawa barin Najeriya saboda zargin satar dukiyar Gwamnati a lokacin su na kan mulki.
Tsohon Gwamna na Sokoto yace babu Kotun da ke binciken sa a halin yanzu domin tuni an wanke sa. Attahiru Bafarawa yace sai da aka yi fiye da shekaru 10 ana shari’a da shi a Kotu kuma har ta kai a karshe an gane bai da laifin komai.
KU KARANTA: Bidiyon karbar daloli: Gwamna Ganduje ya garzaya kotu
Bafarawa a lokacin da yake wata hira da ‘Yan jarida jiya Ranar Lahadi, ya fadi cewa Shugaba Buhari bai isa ya hana sa fita daga Najeriya da sabon kudirin da ya kawo mai lamba ta shida E06 wanda za ta haramtawa wasu barin kasar nan.
Alhaji Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa tun farkon 2018 ne Alkalin wani babban Kotu ya wanke sa daga zargin da ke kan sa kuma har gobe babu kayan sa da Kotu ta karbe domin ba a same shi da aikata rashin gaskiya ba a gaban shari’a.
Jiya dai kun ji Fadar shugaban kasa ta musanta rahoton dake yawo na cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari ta hana wasu manyan mutane har 50 fita daga Najeriya saboda tuhumar da ke kan su a Kasar,
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.
Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng