Yankin Yarabawa na lasar baki, bayan da kabilar Ibo suke ja-inja kan fitowar Obi a mataimakin Atiku

Yankin Yarabawa na lasar baki, bayan da kabilar Ibo suke ja-inja kan fitowar Obi a mataimakin Atiku

- Zaben Peter Obi da Atiku Abubakar yayi a matsayin mataimaki ya kawo cece ku ce tsakanin shuwagabannin kudu maso gabas

- Ba a nemi shawarar shuwagabannin yankin ba kafin a zabe shi

- Cigaban ya ci karo da yarjejeniyar da sukayi da farko

Yankin Yarabawa na lasar baki, bayan da kabilar Ibo suke ja-inja kan fitowar Obi a mataimakin Atiku

Yankin Yarabawa na lasar baki, bayan da kabilar Ibo suke ja-inja kan fitowar Obi a mataimakin Atiku
Source: Twitter

Zaben Peter Obi, a matsayin mataimakin Atiku Abubakar, Dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya kawo cece ku ce tsakanin shuwagabannin kudu maso gabas.

David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, yace ba a nemi yardar shuwagabannin yankin ba kafin zubar Obi.

Yace cigaban yaci Karo da yarjejeniyar da shuwagabannin yankin sukayi na cewa su zasu zabi wanda za'a ba duk wani matsayi a yankin.

Umahi, Chiyaman din kungiyar gwamnonin kudu maso gabas yace an ware shuwagabannin da gwamnonin yankin. Yace duk matsayin da za'a bada a yankin sai masu ruwa da tsakin kudu maso gabas sun amince.

Gwamnan yace bashi da damar hana Obi, amma fa dole ne PDP tayi abinda ya dace.

Umahi da wasu shuwagabannin inyamurai zasuyi taro akan hakan kuma akwai yuwuwar su hana zaben Obi da akayi a matsayin mataimakin.

DUBA WANNAN: Saudiyya ce ta kashe Khasshoggi

A halin yanzu, kudu maso yamma zasu iya kawo nasu gwarzon in har shuwagabannin inyamurai suka kasa samun matsaya.

Kudu maso yamma da kudu maso gabas ne dama yankunan da ake tsammanin samo wanda zai zamo mataimakin Atiku Abubakar din.

Atiku yace ya zabi Obi ne saboda ilimin shi da gogewar shi, tare da zama kwararre ta harkar kudi da tattalin arziki, wanda Najeriya take matukar bukata.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel