Abubuwan da Obasanjo ya taba kiran Atiku dasu tun bayan batawarsu shekaru 15 da suka wuce

Abubuwan da Obasanjo ya taba kiran Atiku dasu tun bayan batawarsu shekaru 15 da suka wuce

- Tsohon shugaban kasar ya dau alwashin qila goyon bayan Atiku tare da jifan shi da munanan maganganu marasa dadin ji

- Amma katsam a ranar Alhamis sai gasu sun sasanta tare da hade kansu. Kadan daga cikin munanan maganganu da tsohon shugaban ya dinga jifan mataimakin nashi da su sune

Abubuwan da Obasanjo ya taba kiran Atiku dasu tun bayan batawarsu shekaru 15 da suka wuce
Abubuwan da Obasanjo ya taba kiran Atiku dasu tun bayan batawarsu shekaru 15 da suka wuce
Asali: Getty Images

A ranar Alhamis ne tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya nuna goyon bayan shi ga tsohon mataimakin shi Atiku Abubakar

"Ubangiji ba zai yafe min ba Idan na goyi bayan Atiku. Yaya za'ayi ma in goyi bayan Atiku? Akan mene?"

Da wadannan kalaman na tsohon shugaban kasan, a ranar Alhamis kuma yayi mubaya'a ga Atiku, shin tsohon ya shirya karbar tsinuwar Ubangiji ne?

DUBAN WANNA: Aljannu dubunnai sun karbi darikar Tijjaniyya

Abubuwan da Obasanjo ya taba kiran Atiku dasu tun bayan batawarsu shekaru 15 da suka wuce

"Matsayata game da Atiku bazata canza ba. Nasan Atiku sosai, kuma na sanar da Matsayata game dashi, bazan canza ba."

"Mara kunyan makaryaci" A littafin manomin mai suna"My Watch " ya kira mataimakin nashi da makaryaci sakamakon cewa da yayi tsohon shugaban kasar na yunkurin juya kundin tsarin kasar nan domin ya dawwama a mulki.

Wannan ya nuna cewa babu bambanci tsakanin Atiku da Baban Iyabo tunda da ya karbi Atikun da hannu bibbiyu.

"Atiku barawo ne, domin sunan shi na cikin sunayen da hukumar yaki da rashawa ta bayyana daga rahoton cibiyoyin shari'a na UK da USA."

Ga dai wuri ga mai waina, a halin yanzu watanni suka rage zuwa zaben 2019, zamu gani, shin wannan hadin kai tare da goyon bayan zai iya ture shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kujerar shugabancin kasa ko a'a?

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel