Dalibai 100,000 ne rikicin tsakiyar Najeriya na manoma/makiyaya ya shafa

Dalibai 100,000 ne rikicin tsakiyar Najeriya na manoma/makiyaya ya shafa

- Sama da dalibai 100,000 ne suka bar makaranta a hargitsin fulani makiyaya

- Hargitsin ya kawo rushewar ajujuwan makarantu sakandire

- An roki Gwamnatin tarayya da ta kawo dauka gurin gyara makarantun da Karo malamai

Dalibai 100,000 ne rikicin tsakiyar Najeriya na manoma/makiyaya ya shafa

Dalibai 100,000 ne rikicin tsakiyar Najeriya na manoma/makiyaya ya shafa
Source: Depositphotos

Zababben sakataren hukumar koyarwa ta Benue, Dr. Wilfred Uji, a jiya ya bayyana cewa sama da daliban sakandire 100,000 ne suka bar makaranta sakamakon sabon hargitsin fulani makiyaya a jihar tun daga watan Janairu.

Uji ya bayyana hakan ne a kaddamar da ofisoshin TSB da akayi jiya a Makurdi. Yace hargitsin ya jawo rushewar makarantun sakandire da yawa a kananan hukumomi Guma da Logo na jihar.

Yace "Wasu daga cikin rusassun makarantun sun hada da GPS Daudu, GSS Gbajimba, GSS Tartyoh, da sauransu. Fulani makiyaya sun kone makarantun kurmus.

Sakataren ya roki Gwamnatin tarayya da ta kawo dauki gurin gyara makarantun sakandire na jihar. Jihar ma tana da bukatar malamai.

DUBA WANNAN: Abiola ne ya yasar damu, ba mu muka munafunce shi ba

"Zamu so karin akalla malamai 4,000 akan wadanda muke dasu a halin yanzu. "

A jawabin kwamishinan ilimi, kimiyya da Fasaha na jihar, Farfesa Dennis Ityavyar, yace Gwamnatin jihar ta kammala shirye shiryen maida makarantun missionaries ga masu su.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel