'Yan Majalisar tarayya 272 da ba bu lallai su koma kujerun su a 2019

'Yan Majalisar tarayya 272 da ba bu lallai su koma kujerun su a 2019

Binciken jaridar The Punch ta yau Asabar ya tabbatar da cewa akwai kimanin Sanatoci 20 da kuma 'Yan Majalisar wakilai 252 da ba bu lallai su koma kan Kujerun su na majalisar tarayya a yayin babban zabe mai gabatowa na 2019.

'Yan Majalisar tarayya 272 da ba bu lallai su koma kujerun su a 2019
'Yan Majalisar tarayya 272 da ba bu lallai su koma kujerun su a 2019
Asali: Twitter

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, mafi akasarin 'yan majalisar sun samu tagarda gami mugun tuntube bisa hanya musamman na jam'iyyar APC da kuma jam'iyyar adawa ta PDP, da suka rasa samun tikitin takara yayin zabukan fidda gwanayen takara na jam'iyyu daban-daban da aka gudanar makonni kadan da suka gabata a kasar nan.

Wani binciken kuma ya tabbatar da cewa, wasu daga cikin wadanda ba za su samu damar komawa Kujerun su ba ya bayu ne a sakamakon neman takarar kujerun gwamna a jihohin su yayin da wasu kuma janye takara da manufa ta su ta karan kansu.

A yayin a halin yanzu akwai dabarwa da ta biyo bayan zabukan fidda gwanayen takara na wasu jam'iyyun, wasu daga 'yan Majalisar na ci gaba da fata gami da kyautata zato da kuma sa rai na samun tikitin takarar ta hanyar tuntube-tuntube da kulla yarjejeniya.

Sanatocin da tuni suka fara bankwana da majalisar dattawa sakamakon shan kasa na rashin samun tikitin takara na jam'iyyun su sun hadar da; Aliyu Sabi-Abdullahi na jihar Neja, Fatimah Raji-Rasaki ta jihar Ekiti, Gbenga Ashafa na jihar Legas, David Umaru na jihar Neja, da kuma Ibrahim Kurfi na jihar Katsina.

KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta nada sabon kakakin ta

Sanatocin kuma da akan iya cewa sun biyu babu yayin da Hausawa kan ce wurin neman Gira ake rasa Idanu sakamakon rashin sa'a ta samun tikitin takarar kujerun gwamna na jihohin su sun hadar da; Baba Kaka Garbai na jihar Borno, Kabiru Marafa na jihar Zamfara, Abubakar Kyari na jihar Borno, Shaaba Lafiagi na jihar Kwara da kuma Sam Anyanwu na jihar Imo.

Wadanda kuma santsi na sa'a ya debe su suka samu tikitin jam'iyyun su na takarar kujerun gwamna sun hadar da; Sunny Ogbuoji na jihar Ebonyi, John Enoh na jihar Cross River da kuma Jeremiah Useni na jihar Filato.

Sai kuma Sanatocin da suka janye takararsu ta kujerun Majalisar dattawa sun hadar da; Adesoji Akanbi na jihar Oyo, Ben Murray Bruce na jihar Bayelsa, Bukar Abba Ibrahim na jihar Yobe, Gbolahan Dada na jihar Ogun da kuma David Mark na jihar Benuwe.

Akwai kuma Sanatoci da kawowa yanzu ba su tabbaci kan makomar su ta samun tikitin takara da har ila yau dambarwa siyasa ta biyo bayan zabukan tsayar da 'yan takara na jihohin su da suka hadar da; Shehu Sani na jihar Kaduna, Lanre Tejuoso na jihar Ogun da kuma Magnus Abe na jihar Ribas.

Sanata Jonah Jang na jihar Filato ya sha kasa yayin neman tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, inda takwaransa na jihar Joshua Dariye, ya ke ci gaba da bai wa diga-digansa hutu a gidan kaso sakamakon laifin mummunar rashawa da ya aikata.

A farfajiyar Majalisar wakilai kuma akwai kimanin 'yan majalisar 252 cikin 300 da a halin yanzu ana iya cewa sun fara bankwana da kujerun su inda mafi akasarin su suka yi rashin sa'a yayin zabukan fidda gwanaye na jam'iyyunsu.

Wasu daga cikin 'yan majalisar da ba za su koma kujerun su ba ya bayu ne a sanadiyar neman wasu kujerun siyasa na daban da suke hankoro, yayin da wasu daga cikin su lamarin ya zamto tamkar sun gaji da wakilcin al'ummomin su da ko kulawa ba su yi ba na sayen takardun takara.

'Yan Majalisar wakilan da ba za su koma kujerun su ba sun hadar da; Mataimakin kakakin majalisar Yussuf Lasun, da ya fita neman kujerar gwamnatin jihar sa ta Osun amma ya sha kashi yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar.

KARANTA KUMA: Zan yi sakayya mai kyawu ga wadanda suka nemi tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP - Atiku

Sauran 'yan majalisar da tun a yanzu sun fara tattara komatsansu sun hadar da; Binta Bello ta jihar Gombe, Orker Jev na jihar Benuwe, Zakari Muhammad, Betty Apiafi da kuma Evelyn Oboro da duk suka lashe tikitin takara na majalisar dattawa na jam'iyyu a jihohin su. Sai kuma Mista Razak Atunwa da ya lashe tikitin takarar kujerar gwamnatin jihar Kwara.

Akwai kuma Mista Pally Iriase na jihar Edo da bai ko kula ba da sake neman kujerar sa yayin da wasu dama da janye takara ko kuma suka yi rashin sa'a ta samun tikitin takara da suka hadar da 'yan majalisa 18 na jam'iyyar APC masu wakilcin mazabu na jihar Legas.

A jihar Kano kuma, 'yan majalisar da dama sun yi hannun riga da sa'a yayin zabukan fidda gwanaye, sai dai shugaba na majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa ya lashe tikitin takarar kujerar sa.

Wasu daga shahararrun 'yan majalisar da ba su samu nasara ba yayin zabukan fidda gwanayen takara na jam'iyyun sun hadar da; Dickson Tarkighir na jihar Benuwe, Sunday Karimi na jihar Kogi, Emmanuel Udendi na jihar Benuwe, Emeka Ujam na jihar Enugu da kuma Hassan Saleh na jihar Benuwe.

A yayin tuntubar jagoran kwamitin watsa bayanai na majalisar, Abdurrazak Namdas, ya bayyana cewa adadin 'yan majalisar wakilai da ba bu lallai su koma kan kujerun su bai kai 252 ba.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng