Yadda Atiku da El-Rufai suka yi rikici kan kudin gudummawar takarar Buhari

Yadda Atiku da El-Rufai suka yi rikici kan kudin gudummawar takarar Buhari

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, sun hade da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufai a wani shirin gidan rediyo

- Sun hadu ne a wani shiri mai suna "Dimokaradiyya a yau" wanda muryar Amurka ta shirya

- Atiku ya bar APC ne saboda jam'iyyar da gwamnoni sun amince da zarcewar Buhari

Yadda Atiku da El-Rufai suka yi rikici kan kudin gudummawar takarar Buhari
Yadda Atiku da El-Rufai suka yi rikici kan kudin gudummawar takarar Buhari
Asali: UGC

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, sun hade da Malam Nasiru Elrufai a wani shiri na gidan rediyo don warware wasu maganganu na jam'iyyar PDP da APC.

Mutanen biyu sunyi Karo ne a shirin "Dimokaradiyya a yau" wanda gidan rediyon muryar Amurka ta shirya a sashen ta na hausa.

Sunyi magana ne akan dalilin da Atiku ya bar APC da kuma cewa Atiku ne ya dau nauyin yakin neman zaben Buhari a 2015.

A cewar Elrufai, Atiku ya bar jam'iyyar APC ne saboda ya gane jam'iyyar da gwamnoni sun amince da zarcewar Buhari a 2019.

DUBA WANNAN: Boka ya kashe mayya

Idan zamu tuna Atiku yace saboda Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi watsi dashi ne duk da rawar ganin da ya taka a yakin neman zabe a 2015.

Amma Elrufai ya kalubalanci Atiku da ya bada shaidar tallafin kudi da yake ta ikirarin ya bada yayi yakin neman zaben Buhari a 2015.

Kamar yanda yace, Atiku ya bar APC ne saboda dalilin kanshi ba wai Don dalilan da ya zayyano ba.

Elrufai yace koda Buhari ba zai tsaya a 2019 ba, toh jam'iyyar bazata ba Atiku tikitin neman shugabancin kasa ba saboda tsohon gwamnan Kano kuma Sanata a yanzu Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ne yake biye da Buhari a zaben fidda gwani a 2015.

"Mu a APC mun dade da sanin cewa Atiku zai bar jam'iyyar zuwa PDP, mun kuma godewa Ubangiji da yasa ya bar jam'iyyar, "Inji Elrufai.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel