Rusau: Dangote ya rushe gidaje da bishiyun wani kauye, hoto

Rusau: Dangote ya rushe gidaje da bishiyun wani kauye, hoto

Hankulan mazauna karamar hukumar Awe a jihar Nasarawa ya tashi bayan kamfanin Dangote na sukari ya rushe gidaje da bishiyoyi masu daraja a alkaryar Akoh dake yankin Tunga.

Rahotanni sun bayyana cewar mahukuntan kamfanin ne su ka dira yankin da manyan motocin rusau tare da fara rushe dukkan gidaje da bishiyoyin yankin bisa dalilin cewar kamfanin sukarin ne ya mallaki dukkan yankin. An yi kiyasin cewar kamfanin ya rushe gidaje da bishiyoyi na miliyoyin Naira.

Da yake magana da manema labarai a yankin Akoh, na 'yan kabilar Tiv, da ke kan iyaka jihar Benuwe, Honarabul Francis Yua, mai taimakawa gwamna Tanko Almakura na jihar Nasarawa a bangaren raya karkara, ya ce basu da masaniya a gwamnatance cewar kamfanin ya sayi wurin da ya rushe.

Rusau: Dangote ya rushe gidaje da bishiyun wani kauye, hoto
Dangote ya rushe gidaje da bishiyun wani kauye
Asali: Twitter

Yua, wanda shi ma dan asalin wannan yanki ne, ya bayyana rusau din da kamfanin ya yi a matsayin haramtacce tare da bayyana cewar idan har kamfanin ya sayi wurin kamar yadda ya yi ikirari, kamata ya yi ya bi tsarin doka na biyan jama'ar dake zaune a yankin diyya.

Rusau: Dangote ya rushe gidaje da bishiyun wani kauye, hoto
Rusau dinDangote a Tunga
Asali: Twitter

Dagacin garin Akoh, Zaki Michianan, ya ce ba su da masaniyar kamfanin ya saye kauyen nasu, kawai ganin jami'an kamfanin su ka yi sun zo da manyan motocin aiki sun fara rushe masu gidaje da bishiyoyi.

Kazalika sarkin Tunga, Alhaji Muhammed Ibrahim, ya ce kamfanin ya aikata babban kuskure.

Rusau: Dangote ya rushe gidaje da bishiyun wani kauye, hoto
Dagacin garin Akoh, Zaki Michianan
Asali: Twitter

Da jaridar Daily Trust ta tuntubi jami'in hulda da jama'a na kamfanin sukarin Dangote dake Tunga, Sa'idu Muhammed, ya ce kamfanin ba shi da masaniya a kan rusau din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel