Canja dan takarar gwamnan PDP a Kano: Masoya Kwankwaso sun fara kona katinansu na PDP, hotuna

Canja dan takarar gwamnan PDP a Kano: Masoya Kwankwaso sun fara kona katinansu na PDP, hotuna

Labarai da ke dakin watsa labarai na Legit.ng sun tabbatar da cewar mambobin PDP, tsagin Kwankwasiyya, a jihar Kano sun fusata tare da fara kona katinsu na jam'iyyar saboda canja sunan Abba K. Yusif, dan takarar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, tare da maye shi da na tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Malam Salihu Sagiru Takai.

A dazu, da rana, ne kafafen yada labarai da su ka hada da Legit.ng su ka wallafa rahoton cewar jam'iyyar PDP ta canja sunan Abba K. Yusif, surukin Kwankwaso, da na Malam Sagiry Takai.

Legit.ng ta rawaito cewar jam’iyyar PDP ta yi watsi da dan takararta Abba K Yusuf, na kujerar gwamnan jihar Kano, kuma surukin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tare da tabbatar da Malam Salihu Sagir Takai a matsayin sabon dan takararta a zaben 2019.

Canja dan takarar gwamnan PDP a Kano: Masoya Kwankwaso sun fara kona katinansu na PDP, hotuna
Masoya Kwankwaso sun fara kona katinansu na PDP
Asali: Facebook

Canja dan takarar gwamnan PDP a Kano: Masoya Kwankwaso sun fara kona katinansu na PDP, hotuna
Masoya Kwankwaso sun fara kona katinansu na PDP
Asali: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito uwar jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba biyo bayan nuna rashin amincewa da sauran yan takarar gwamna a jam’iyyar suka nuna game da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani a gidan Kwankwaso.

DUBA WANNAN: 2019: Obasanjo ya yafewa Atiku, ya kira shi sabon shugaban kasar Najeriya mai jiran gado

Kazalika majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewar Takai ya samu goyon bayan shuwagabannin jam’iyyar PDP na kananan hukumomin 38 daga cikin 44 da ke jihar Kano a wani kwarya kwaryan taro da aka yi a Abuja.

Sai dai wannan mataki na uwar jam'iyyar PDP bai yiwa masoya da masu goyon bayan Kwankwaso dadi ba, hakan ne kuma ya sa suka fara kona katinansu na zama mambobin jam'iyyar tare da saka hotunan a shafukan sada zumunta dake yanar gizo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel