Matsalar takardun karatu: Majalisa ta ki tantance mutumin da Buhari ya tura

Matsalar takardun karatu: Majalisa ta ki tantance mutumin da Buhari ya tura

A yau ne Majalisar Dattawa da sanar da rashin amincewarta da nadin Dr. AbdulMalik Mohammed Durnguwa a matsayin kwamishina a Hukumar Kidaya na Kasa (NPC).

Durnguwa yana daya daga cikin mutane 23 da gwamnatin tarayya ta turawa majalisar domin tantancesu a matsayin kwamishinoni a NPC.

A yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin a zaman majalisa da akayi a yau Alhamis, Sanata Suleiman Hunkuyi ya ce "Majalisar ba ta tantance Dr. AbdulMalik Mohammed Durnguwa saboda matsalar takurdun karatu".

Matsalar takardun karatu: Majalisa ta ki tantance mutumin da Buhari ya tura
Matsalar takardun karatu: Majalisa ta ki tantance mutumin da Buhari ya tura
Asali: UGC

A yayin da shi kuma Sanata Ali Ndume ya ce aikin kwanitin ne ta tabbatar da cewar dukkan wadanda za a yiwa nadin sun cika ka'idojin da doka ta tanada, takwararsa Sanata Sam Egwu ya ce an kwashe kusan mako daya ana tantancewar saboda haka ba za'a karawa Durnguwa wani wa'adi ba.

DUBA WANNAN: Buhari ya sanya hannu kan dokar hana karkatar da kudi kasashen waje da kaucewa biyan haraji

Sanata Gumel Abdullahi ya ce majalisar ba ta gamsu cewar Mohammed Durnguwa ya rubuta jarabawar kammala sakandire ta Senior School Certificate Examination (SSCE) ba.

Mataimakin shugaban majalisa, Ike Ekweremadu ya bayar da shawarar cewar kwamitin da tafi ta gudanar da bincike cikin makonni hudu kana sannan ta dawo ta bayar da rahoto.

Wadanda aka tantance sun hada da Nwanne Nwabuisi, Dr. Clifford T.O. Zirra, Dr. Chidi Christopher Ezeoke, Barr. Isa Audu Buratai, Navy Captain Charles Iyam Ogwa, Sir Richard Odibo, Okereke Darlington Onuabuchi, Mr. A.D. Olusegun Aiyejina, Ejike Ezeh, Hon. Abubakar Mohammed Danburam, Prof. Uba S.F. Nnabue da Suleiman Ismaila Lawal.

Sauran sune Professor Jimoh Habibat Isah, Dr. Sa'adu Ayinla Alanamu, Nasir Isa Kwarra, Barr. Aliyu Datti, Yeye (Mrs.) Seyi Adereinokun Olusanya, Prince (Dr.) Olanadiran Garvey Iyantan, Senator Mudasiru Oyetunde Hussain, Mrs. Cecillia Arsun Dapoet, Dr. Ipalibo Macdonald Harry da Sale S. Saany

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel