Principal ta kwace malaman gwamnati na N-Power ta kai makarantarta

Principal ta kwace malaman gwamnati na N-Power ta kai makarantarta

- Wata shugabar makaranta ta maida malamai da gwamnati ta tura zuwa makarantar ta mai zaman kanta

- Wani malami yace gwamnati ta turo musu malamai amma shugabar makarantar ya turasu makarantar ta mai zaman kanta

- Makarantar tana fama da karancin malamai da ajujuwa

Principal ta kwace malaman gwamnati na N-Power ya kai makarantarsa
Principal ta kwace malaman gwamnati na N-Power ya kai makarantarsa
Asali: UGC

Shugabar makarantar Asero high school Abeakuta jahar Ogun Mrs A.Ogunsade ta nuna son zuciyar ta.

Bisa tsarin da gwamnati ta kafa na N.power ta tura malamai 14 zuwa makarantar ta Asero duba da karancin malamai da suke fama dashi.

Mrs Ogunsade ta kwashe wadannan malamai inda ta maidasu makarantar ta mai zaman kanta.

DUBA WANNAN: Shugaban kasa na da damar kwace kadarori da aka samu ta hanyar haramun - Kotu

Wani malami wanda yaji tsoron a bayyana sunan sa yace gwamnati ta kawo musu malamai 14 inda ita kuma shugabar su ta kwashe su ta maidasu zuwa makarantar ta kuma gwamnati ce take biyan su albashi.

Domin tabbatar da wannan zargi munyi kokarin zantawa da ita shugabar makarantar amma saita bayyana mana cewa bata gari.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel