2019: Ba bu tasirin da Taron Dangi zai yi akan Buhari - Femi Adesina

2019: Ba bu tasirin da Taron Dangi zai yi akan Buhari - Femi Adesina

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, fadar shugaban kasa ta cika baki gami da bugun kirji wajen hararo nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zabe na 2019 da cewar ya zamto wani muruci na kan dutse.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne hadimin shugaban kasa kan hulda da manema labarai, Mista Femi Adesina, ya bayyana cewa ba bu wani tasiri da taron dangi na 'yan adawa zai yi ga nasarar shugaba Buhari a yayin zabe na 2019.

A cewar sa, 'yan adawa masu taron dangi na ganin shugaba Buhari ya sha kasa yayin babban zabe za su sha mamaki domin kuwa ba bu shakka shi zamto zakara da nasara ke sanya sawunta a duk inda ya cire nasa.

Mista Adesina ya bayyana hakan ne a shafin sa na dandalin sada zumunta, wanda wannan sako ya yi daidai da ranar yau ta Alhamis da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya karbi bakuncin mataimakin sa, Atiku Abubakar da ya ziyarce sa a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Femi Adesina
Femi Adesina
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, ya yi wata muhimmiyar ganawa da Ubangidansa tare da wasu jiga-jigai na jam'iyyar PDP dangane da zaben 2019.

Ganawar kamar yadda rahotanni suka bayyana ta sake kulla dankon zumunci tsakanin jiga-jigan biyu, inda Obasanjo ya bayyana murna tare da goyon baya ga Atiku kasancewarsa marikin tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Wata Tsohuwar Gada da ta shekara 51 ta zagwanye a jihar Taraba

A makon da ya gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP yayin zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, a sanadiyar wannan lamari dangane da yadda al'amurran siyasa ke sauyawa da wasu jiga-jigan kasar nan da dama ke bayyana goyon bayan su ga Atiku, ya sanya fadar shugaban kasa ta mayar da martani da cewar shugaba Buhari ya zamto tamkar murucin kan dutse da taron dangi ba zai tasiri gare sa ba.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel