Wata Tsohuwar Gada da ta shekara 51 ta zagwanye a jihar Taraba

Wata Tsohuwar Gada da ta shekara 51 ta zagwanye a jihar Taraba

Tsautsayi dai da Hausawa kan ce ba ya wuce ranarsa ya auku da sanyin safiyar ranar Larabar da ta gabata yayin da wata Gada mahadar garuruwan Wukari da Takum da zagwanye a yankin Peva dake jihar Taraba a Arewacin Najeriya.

Ko shakka ba bu garin Takum nan ce mahaifar tsohon Ministan tsaro kuma tsohon shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Janar Theophilus Danjuma.

Wani mashaidin wannan lamari, Mista Torsaa Chieve, da ya zanta da manema labarai na jaridar The Punch ya bayyana cewa, babbar gadar ta zagwanye a sakamakon saukar ruwan sama mai tsananin gaske har na tsawon sa'o'i dama a yankin.

Ya bayyana takaicinsa dangane da yadda a baya can al'ummar yankin suka sha fama wajen kiran gwamnatin tarayya akan ta kawo dauki na gyaran gadar da zamto wani tarkon mutuwa tun gabanin saukar damina a bana.

Wata Tsohuwar Gada da ta shekara 51 ta zagwanye a jihar Taraba
Wata Tsohuwar Gada da ta shekara 51 ta zagwanye a jihar Taraba
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan gada ta shafe tsawon shekaru 51 tun yayin da aka assasa ta tare da gina ta a shekarar 1967 a zamanin mulkin soji na Janar Yakubu Gowon, yayin da Janar Olusegun Obasanjo ya kasance mai lura da kwangilar gina ta.

KARANTA KUMA: Saukar ruwan sama mai tsanani ta yi awon gaba da wani 'Dalibi dan shekara 11 a jihar Calabar

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, an gina wannan katafariyar gada ne domin bai wa dakarun soji dama ta samun hanyar zuwa Barikin Soji na Ada dake garin Takum.

Kazalika jaridar Legit.ng ta samu rahoton cewa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya taya murna ga Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin sa da ya lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP yayin zaben fidda gwani da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel