Gwamnatin Saudiyya ta kaddamar da manyan jirgin kasa na zamani daga Makka zuwa Madina

Gwamnatin Saudiyya ta kaddamar da manyan jirgin kasa na zamani daga Makka zuwa Madina

Wasu sababbin jiragen kasa na zamani masu gudun walkiya zasu fara zarya a tskanin birnin Makkah da birnin Madina, tafiyan kilomita dari hudu da hamsin (450km) cikin mintuna casa’in gaba daya, kamar yadda kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Kirkirar wannan jirgi ya zamto wani hanyar da gwamnatin kasar Saudiya take bi na ganin ta sauya akalar samar da kudaden shiga daga man fetir zuwa sufuri, da ma wasu hanyoyi na daban, wannan jirgi zai dinga shafe kilomita dari uku cikin kowanne awa.

KU KARANTA: Rundunar Yansandan Najeriya ta garkame wani dan majalisan wakilai

Gwamnatin Saudiyya ta kaddamar da manyan jirgin kasa na zamani daga Makka zuwa Madina
Jirgin
Asali: Twitter

Haka zalika jirgin zai ratsa biranen har zuwa bahar maliya, inda tashar jirgin rawu na biyu mafi girma a kasar yake, watau tashar jirgin ruwa ta tunawa da Sarki Abdullahi, sa’annan za dauki adadin fasinja miliyan uku a duk shekara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sarkin Saudi, Salmaan ne ya kaddamar da jirgin a watan Satumbar bana inda ta fara tashi daga garin Jidda zuwa Madina, inda yace an kaddamar da jirgin ne don rage ma mahajjata wahalhalun tafiya daga Makka zuwa Madina.

Gwamnatin Saudiyya ta kaddamar da manyan jirgin kasa na zamani daga Makka zuwa Madina
Jiragen
Asali: Twitter

Sanannen lamari ne cewa miliyoyin musulmai ne suke tafiya kasar Makka domin aikin Hajj, inda suke gudanar da bauta a babban masallacin Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, tare da zagaye dakin Allah wato Ka’abah, da ziyarar kabarin Manzon Allah.

Wannan jirgi na daya daga cikin kokarin da kasar Saudiya ke yin a ganin ta bude kasarta ga yan kasuwannin kasashe waje don su zuba hannaye jari a kasar zuwa shekarar 2030, haka zalika manufar wannan tsari shine sauya hanyoyin samun kudaden shiga ga gwamnatin kasar daga man fetir.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng