An kashe soja guda, anyi garkuwa da wata Mata a jihar Filato

An kashe soja guda, anyi garkuwa da wata Mata a jihar Filato

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, an tabbatar da salwantar rayuwar wani sojan kasa yayin da wasu 'yan tadda rike da bindigu suka samu nasarar yin garkuwa da wata Matashiya, Hafsat Gambo, mai shekaru 21 a duniya.

A sakamakon aukuwar wannan mummunan al'ajabi a ranar Talatar da ta gabata, rayuwar wani karamin ma'aikacin soja da aka bayyana sunansa a matsayin Abdullahi S. ta zo karshe yayin da 'yan ta'adda suka harbe shi da harsashi na bindiga.

Wannan tsautsayi ya ritsa da sojan a unguwar Kwanar Soja dake birnin Jos na jihar Filato, inda 'yan ta'addan suka harbe shi yayin tserewa bayan sun gama cin Karen su ba bu babbaka.

An kashe soja guda, anyi garkuwa da wata Mata a jihar Filato
An kashe soja guda, anyi garkuwa da wata Mata a jihar Filato
Asali: Facebook

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Mathhias Tyopev, shine ya tabbatar da aukuwar wannan lamari sai dai ya bayyana cewa ba bu wanda ya shiga hannu a halin yanzu da bincike ke ci gaba da gudana.

KARANTA KUMA: An cafke ma'aikatan hukumar NDLEA na bogi a jihar Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari na ta'addanci ya gudana ne da misalin karfe 7.50 na yammacin ranar 9 ga watan Oktoba, inda wani Mutum na gari, Alhaji Idris Gambo yayi gaggawar shigar da korafi zuwa ga hukumar 'yan sanda.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hadimin gwamnan jihar Akwa Ibom kan harkokin zabe, Mfon Ndume, ya fara shirye-shiryen kwancewa Ubangidansa zani a kasuwa.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel