Kungiyar OPC sun yaba da zabar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a PDP

Kungiyar OPC sun yaba da zabar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a PDP

- Kungiyar Yarbawa sun yaba da zabar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a PDP

- A cewar shugaban kungiyar PDP tayi zabe mai kyau

- Hakazalika a bangaren kungiyar Buhari sun ce shugaban kasar zai kayar da Atiku cikin sauki

Wata kungiyar Yarbawa mai suna O’dua People’s Congress (OPC) sun yaba ma billowar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019.

Kungiyar OPC sun yaba da zabar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a PDP
Kungiyar OPC sun yaba da zabar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a PDP
Asali: Original

A wata sanarwa daga shugaban kungiyar, Dr. Frederick Fasehun, yace babban taron PDP da aka gudanar a Port Harcourt, jihar Rivers a karshen makon da ya gabata sunyi zabe mai kyau wajen zabar Atiku a matsayin dan takarar ta.

A bangare guda kuma kungiyar Re–elect Buhari Movement (RBM) ta taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar tsayar das hi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi.

A cewar kungiyar Buhari na da damar kayar da Atiku a zabe mai zuwa ba tare da wani wahala ba.

KU KARANTA KUMA: IGP Idris ya ki amincewa da shirin hukumar yan sanda na rage ma jami’ai 1,500 matsayi

A sanarwa daga shugabanta, Emmanuel Umohinyang, ya bayyana tsayar da Buhari a matsayin sakamakon kyawawan ayyukan da yayi a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng