Rahoto: Duk da tawayar tattalin arziki, ashe har yanzu Najeriya ce ta daya a Afirka

Rahoto: Duk da tawayar tattalin arziki, ashe har yanzu Najeriya ce ta daya a Afirka

-Forbes Africa, tace Najeriya ce kasa mafi kyan tattalin arziki a Afirka

-Najeriya ta doke kasar Afirka ta kudu, kasar Egypt da sauran su

-Kasar Madagascar ce ta 10 a jerin kasashe mafi kyan tattalin arziki a Afirka

Rahoto: Duk da tawayar tattalin arziki, ashe har yanzu Najeriya ce ta daya a Afirka
Rahoto: Duk da tawayar tattalin arziki, ashe har yanzu Najeriya ce ta daya a Afirka
Asali: UGC

Forbes Africa, wata masana'antar bincike ta duniya ta bayyana Najeriya a matsayin kasa mafi kyawun tattalin arziki a Afirka a 2018.

Najeriya ta doke kasar Afrika ta kudu, kasar Egypt da sauran su.

Kamar yanda Forbes ta fada, Najeriya ta zo ta farko ne da dala biliyan 172,inda kasar Afrika ta kudu take biye da ita da dala biliyan 166.735.

DUBA WANNAN: Ana sai da birrai daga Najeriya N5m a kasashen waje

Hakazalika kasar Egypt tazo ta uku da dala biliyan 78,Algeria da dala biliyan 66,Libya da dala biliyan 65,Botswana da dala biliyan 22.675, Ghana da dala biliyan 20.458,Morocco da dala biliyan 18,Ivory Coast da dala biliyan 11 sai kasar Madagascar da dala biliyan 6.766.

A kasashen da ke da makwaftaka da Najeriya a yammacin Afirka, Ghana ce ta 6,Morocco ta 8 sai Madagascar ta goma.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel