Neman aron kudi: Kwamitin karbo bashi a Majalisar Dattawa za tayi zama yau – Shehu Sani

Neman aron kudi: Kwamitin karbo bashi a Majalisar Dattawa za tayi zama yau – Shehu Sani

A farkon makon nan ne aka samu labari cewa Gwamnatin Tarayya na neman karbowa Najeriya wani sabon bashi na Dala Biliyan 2.8. Yanzu dai mun ji cewa Majalisa za ta fara zama game da wannan batun.

Neman aron kudi: Kwamitin karbo bashi a Majalisar Dattawa za tayi zama yau – Shehu Sani
Sanatoci za su duba takardar Shugaban kasa na neman karbo sabon bashi
Asali: UGC

Kwamitin da nauyin karbo bashi daga kasar waje ya rataya a kan ta a Majalisar Dattawa ta tabbatar da cewa za tayi zama yau game da batun cin bashin. Shugaban wannan kwamiti Sanata Shehu Sani ya bayyana wannan a jiya.

Sani ‘Dan Majalisar APC na Jihar Kaduna ya tabbatar da cewa a Ranar Alhamis dinnan ne Sanatoci za su duba takardar da Shugaban kasa Buhari ya aikowa Majalisa inda yake neman Najeriya ta karbo wasu bashi daga ketare.

Sanatan yace za su gayyaci Ministar kudi ta Kasar da kuma ofishin DMO mai kula da bashi na Najeriya su yi bayani a gaban kwamitin na Majalisar Dattawan kafin a amince da bukatar karbo aron wannan makudan Dalolin kudi.

KU KARANTA: Buhari ya sanya hannu kan dokar hana karkatar da kudi kasashen waje

Fadar Shugaban kasa ta aikowa Majalisar Dattawa cewa tana neman aro Dala biliyan 2.786 daga waje domin fara biyan kudin manyan ayyuka na kasafin kudin bana. Yanzu dai ana kukan cewa bashin da ke kan Najeriya ya fara yawa.

Sanatan yace Gwamnatin Tarayyar kuma na neman karin wasu Dala Miliyan 82.54 da duk ake sa rai za a kashe wajen biyan kudin kwangiloli. Ana sa rai dai Ministar kudi ta rikon kwarya Zainab S. Ahmed ta hallara gaban ‘Yan Majalisar yau.

Jiya kun ji cewa Alhassan Doguwa ya bayyana cewa babu wani yunkuri da Majalisa ke yi na kokarin tsige Shugaban ta Yakubu Dogara daga matsayin sa saboda ya bar Jam’iyyar APC zuwa PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel