Ana sace birirruka daga Najeriya a sayar N5m a kasashen waje - Bincike
- Ana sayar da birran akalla $12,000 a kasashen waje
- Daga Najeriya ake sato su a fitar waje don masu so
- Gwamnatin Najeriya tace bata yarda ba

Asali: Twitter
Ashe birrai na da tsada, wani sabon rahoto da masu binciken kimiyya da ma kare namun daji suka yi, sun gano yadda masu bin barauniyar hanya da fasa-kwabri ke sato birarruka a dazukan Njeriya don sayarwa a kasuwannin kasashen Turai da Asiya.
A kasashen wajen dai, ana son birrai, inda akan ajje su a matsayin abokan zaman gida, wasannin kayatarwa, ko kuma a cinye su.
Gwamnatin Najeriya dai, bayan samun labarin, tace a dawo mata da duk birran da aka tabbatar na kasar ta ne da aka sace, bayan da BBC ta fasa labarin rahoton.
DUBA WANNAN: Sanatoci zasu hada kai a PDP/APC don tsige su Saraki
Su dai Birrai, dangogi ne na Ape family, wadanda kimiyya ta gano ashe kakanninsu daya da dan-Adam, wanda hakan yasa ake yawan son amfani dasu wajen gwaje-gwajen magunguna kafin a gwada a jikin danAdam, dalilin cewa suna da DNA 99.8% sak da namu.
DNA shi ke hada duk wata halitta a duniya, kkuma sinadarin acid ne mai kunshe da murdaddun nau'in kayan organic molecules.
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng