Sanatocin APC da PDP sun cimma matsaya wajen aiki tare don tsige Saraki da Ikweremadu

Sanatocin APC da PDP sun cimma matsaya wajen aiki tare don tsige Saraki da Ikweremadu

- Sanatocin Najeriya sunyi taro bayan da suka dawo daga hutu

- Sun kai ga matsaya a tsarin tsige shugaban majalisar

- Sun yanke shawarar zama lafiya tare da hana manyan majalisar fadace fadace

Sanatocin AOC da PDP zasu hada kai wajen aikin tsige Saraki da Ikweremadu
Sanatocin AOC da PDP zasu hada kai wajen aikin tsige Saraki da Ikweremadu
Asali: UGC

Sanatocin APC da PDP, a ranar talata, 9 ga watan Octoba, sun kai ga matsaya a shirin tsige shugaban majalisar Bukola Saraki.

Majiyar mu ta ruwaito mana cewa, sun kai ga matsayar ne a wani taron da sukayi na minti 20 bayan dawo daga dogon hutun da sukayi.

Mun samu labari cewa anyi taron ne don magance barazanar da ke tasowa.

DUBA WANNAN: Rahoton EFCC kan Atiku a 2006

An ruwaito cewa yan jam'iyyar APC sunyi amfani da damar wurin samun alkawarin shugaban majalisar cewa ra'ayin kasa zai cigaba da zama jagaba a zauren majalisar. Sun kuma yarje akan cewa bazasu bar wani abu daga waje ba ya dinga kawo hayaniya a majalisar.

A jiya ne muka ruwaito yanda sakataren yada labarai na APC, Yekini Nabena ya hori Sanatocin jam'iyyar dasu gaggauta tsige Bukola Saraki kamar yanda delegates din PDP suka ki zaben shi.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel