Buhari na neman ciwo wa Najeriya sabon bashin tiriliyan daya

Buhari na neman ciwo wa Najeriya sabon bashin tiriliyan daya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci amincewar majalisa gurin karbar sabon bashi

- Za'ayi amfani da kudin ne gurin daukar nauyin wani sashi na kasafin kudin 2018

- Ya kuma bukaci amincewar majalisar akan Naira biliyan 346 na kasafin kudin NDDC

Buhari na neman ciwo wa Najeriya sabon bashin tiriliyan daya
Buhari na neman ciwo wa Najeriya sabon bashin tiriliyan daya
Asali: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci amincewar majalisar dattawa akan sabon rance dala biliyan 2,868,540,000 da yake son yi.

Bukatar tana kunshe ne a wasikar da ya tura ga shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Saraki ya karanta wasikar ne a zauren majalisar a jiya.

Buhari ya bayyana cewa za'ayi amfani da bashin ne gurin tabbatar da wani bangare na kasafin kudin 2018 tare da manyan aiyukan more rayuwa.

DUBA WANNAN: Ashe Ganduje ma barawo ne

Shugaban kasar ya bukaci amincewar majalisar akan Naira biliyan 346 domin kasafin kudin kamashon cigaban Niger Delta na 2018.

Bayanin tsarin kasafin kudin ya nuna Naira biliyan 313.883 za'ayi amfani dasu gurin manyan aiyuka, Naira biliyan 31 kuma domin aiyukan yau da kullum.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel