Wata yar Najeriya ta halaka kanta bayan gwamnatin kasar Ghana ta garkame mata shago

Wata yar Najeriya ta halaka kanta bayan gwamnatin kasar Ghana ta garkame mata shago

Biyo matakin kulle shagunan yan Najeriya mazauna kasar Ghana da gwamnatin kasar ta dauka ya sanya wata mata uwar yaya uku daukan matakin kashe kanta da kanta, kamar yadda kungiyar yan kasuwan Najeriya mazauna Ghana suka tabbatar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyar ta sanar da haka ne a yayin ziyarar da ta kai ma babbar mashawarciyar shugaban kasa Buhari akan al’amuran yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri Erewa a Abuja, inda suka bukaci shugaba Buhari ya shiga maganar.

KU KARANTA: Shekaru 4 ko 8: Al’ummar kudancin Najeriya sun shiga rudani akan zabar Buhari ko Atiku

Shugaban kungiyar, Cif Chukwuemeka Nnaji ya bayyana cewa matar mai suna Stella Ogonna Okaleke ta kashe kanta ne a ranar 22 ga watan Satumba bayan ta gagara cika tsauraran sharuddan da gwamnatin kasar Ghana ta gindaya ma yan kasuwan kafin su bude musu shagunansu.

Nnaji ya roki shugaba Buhari daya shiga cikin maganar, musamman game da batun cin zarafin yan kasuwan Najeriya dake kasar Ghana da hukumomin kasar ke yi, wanda yace a yanzu haka abin ya wuce gona da iri a garin Kumasi.

Da take nata jawabin, Uwargida Abike Dabiri ya bayyana alhinin gwamnatin Najeriya bisa mutuwar wannan yar kasuwa, sa’annan ta mika ta’aziyyar ta a madadin gwamnatin Najeriya ga iyalan matar da ma kungiyar gaba daya.

“Ina tayaku alhinin mutuwar wannan matar, na san akwai zafi, amma ina gareku daku kwantar da hankuklanku, ku zauna lafiya, kuma ina fatan zaku sanar damu lokacin da za’a binneta don mu aika da sakon kwarin gwiwa ga iyalanta.” Inji ta.

A ranar 27 ga watan Yuli ne gwamnatin kasar Ghana ta garkame shagunan yan Najeriya mazauna kasar Ghana, sa’annan ta gindaya sharadin sai kowanne dan kasuwa na da kudi dala miliyan daya za’a bude masa shagonnasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel