Hotuna: Shehu Sani ya amsa kalubalen da El-Rufai ya yi masa na shiga cikin kasuwa

Hotuna: Shehu Sani ya amsa kalubalen da El-Rufai ya yi masa na shiga cikin kasuwa

Sanatan al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya amsa kalubalen da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya jefa masa na cewwa idan ya isa mai jama’a ya shiga cikin kasuwannin jahar Kaduna ya gani.

Gwamnan ya jefa wannan kalubale ne ga Shehu Sani yayin ganawa da manema labaru a ranar Litinin 8 ga watan Oktoba a garin Kaduna, inda yace yana tabbacin idan har Shehu Sani ya shiga kasuwannin Kaduna sai jama’a sun lakada masa dan banzan duka.

KU KARANTA: Shekaru 4 ko 8: Al’ummar kudancin Najeriya sun shiga rudani akan zabar Buhari ko Atiku

Hotuna: Shehu Sani ya amsa kalubalen da El-Rufai ya yi masa na shiga cikin kasuwa
Shehu
Asali: Facebook

“Shehu Sani ba zai iya shiga cikin kasuwan Kaduna don yakin neman zabe ba, na kalubalace shi idan ya isa yazo mu shiga kasuwar mu ga wanda zai fito ba tare da ko kwarzane ba.” Inji gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Sai ga shi a ranar Talata 9 ga watan Oktoba Sanatan ya kutsa kai cikin babbar kasuwan jahar Kaduna ba tare da jami’an tsaro ba, inda shima ya kalubalanci gwamnan da ya koma kasuwar ba tare da jami’an tsaro ba kamar yadda ya yi.

Da yake zagayawa cikin kasuwar, an hangi turururuwan jama’a da yan kasuwa sun yi dafifi sun zagaye Sanatan, wanda suke yi ma kirari da jagoran talakawa, tare da da mukarrabansa a gefe.

Hotuna: Shehu Sani ya amsa kalubalen da El-Rufai ya yi masa na shiga cikin kasuwa
Shehu
Asali: Facebook

Rikicin Gwamna El-Rufai da Sanata Shehu Sani ya samo asali ne tun a shekarar 2015, jim kadan bayan kammala babban zaben shekarar, inda kowannensu ya samu nasarar darewa kujerar da suka tinkaho da shi a yanzu ta hanyar hawa bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan rikici ya kara sabunta ne a daidai lokacin da uwar jam’iyyar APC ta yi watsi da dan takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya wanda ke da goyon bayan gwamnan jahar, Uba Sani, inda tace ta ajiye ma Shehu Sani tikitin takarar wannan kujera ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel