Gwamna Yari ya samu tikitin Sanata a APC a Jihar Zamfara

Gwamna Yari ya samu tikitin Sanata a APC a Jihar Zamfara

Mun samu labari cewa Gwamna Abdulaziz Yari ya lashe tikitin Sanata a Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Zamfara. Gwamna Yari ya karbe kujerar ne hannun Sanata Ahmed Sani Yariman-Bakura.

Gwamna Yari ya samu tikitin Sanata a APC a Jihar Zamfara
An nemi Jam’iyyar APC ta ba Gwamna Yari saki uku
Asali: Facebook

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Zamfara da Uwar Jam’iyya ta kora watau Lawali M. Liman ne Malamin zaben da ya tsaida Alhaji Abdulaziz Yari a matsayin ‘Dan takarar Sanatan Zamfara ta Yamma a zaben 2019.

Sai dai Kwamitin Manjo-Janar Abubakar Mustapha Gana da aka nada a Jihar ta nuna cewa ba za ta yarda da zaben ba. Gwamna Abdulaziz Yari wanda ke shirin barin gado ya samu kuri’u 166,610 ne a zaben na fitar da gwani.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya rubutawa Saraki wasika a Majalisa

Sanata Kabiru Marafa wanda yake wakiltar Zamfara a Majalisar Dattawa ya nemi a kori Gwamna Abdulaziz Yari daga Jam’iyyar APC mai mulki. Sanatan yayi wannan magana ne a shafin sadarwa na zamani na WhatsApp.

Ahmed Yariman-Bakura wanda kusan shi ya kawo Gwamna Yari kan mulki a 2011 ya tafi Sanata ne tun lokacin da ya gama Gwamna a 2007. Yanzu dai ana ta faman rikici tsakanin su Sanata Marafa da Gwamna Yari a Zamfara.

Dazu kun samu labari cewa shugabancin Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara da aka tsige kwanaki ta bayyana cewa Alhaji Mukhtar Shehu Idris ne yayi nasara a matsayin ‘Dan takarar Gwamna a APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel