Bayan bincike, Jami'a ta kori sabbin Farfesoshi har biyu saboda iskanci da mata
- Jami'ar jihar Legas ta kori malamai uku da aka kama da neman dalibai da rashin da'a
- Jami'ar ta amince da karawa malamai 49 matsayi da 200 wadanda basa koyarwa
- Hukumar jami'ar ta nuna rashin amincewar ta da neman dalibai da rashin da'a

Asali: UGC
Hukumar ladaftarwa ta jami'ar jihar Legas ta amince da korar malaman ta guda uku sakamakon lalata da dalibai tare da rashin da'a.
Kwamitin ta yanke hukuncin ne a taron ta na 119 da tayi a ranar Alhamis, 4 ga watan Octoba. Malaman da aka kora sun hada da : Dr. Adubunmi Ayoola Sunkanmi, mai neman zama farfesa a bangaren tattali na jami'ar ; Dr. Ogunwande Isiaka Ajani, mai neman zama farfesa a bangaren Chemistry da Dr. Gbeleyi Emmanuel Orilade, malami a mataki na biyu a bangaren Anatomy.
DUBA WANNAN: Albishirinku makarantaa jaridar NAIJ
Kwamitin ta amince da karawa malamai masu koyarwa 49 da malamai 200 marasa koyarwa zuwa matsayi daban daban.
Hukuncin da hukumar ladaftarwa ta jami'ar ta nuna cewa bazata amince da lalata da dalibai ba da kuma rashin da'a tare da cigaba tabbatar da walwalar malaman da yakamata da dalibai a jami'ar.
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng