Jami’in Soja ya bindige wani yaro ya caka ma Dansanda wuka akan sun hanashi dukan budurwarsa

Jami’in Soja ya bindige wani yaro ya caka ma Dansanda wuka akan sun hanashi dukan budurwarsa

Daga rabon fada wani jami’in Soja ya bindige wani karamin yaro mai suna Jude, sa’annan ya caka ma mahaifin jude wuka, a daren Litinin 8 ga watan Oktoba a wani barikin Yansanda dake garin Maiduguri na jahar Borno inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya sanya fusatattun matasa rufe hanyoyin da suka ratsa ta unguwar tare da banka ma tayoyi wuta don nuna bacin ransu ga kisan da Sojan yayi tare da caka ma jami’in Dansanda wuka.

KU KARANTA: Assha! Hukumar jami’ar jahar Legas ta sallami lakcarori guda 3 akan neman dalibansu

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ana zaune a wani mashaye ne sai jama’a suka hangi wasu mutane uku suna ta dukan wata budurwa tare da kokarin wurgota waje daga cikin Keke Napep, hakan ta sanya jama’an dake wajen suka shiga tsakani suka ceto budurwar.

Ashe shiga tsakanin da jama’an suka yi ya harzuka mutanen uku wadanda jami’an Sojoji ne, nan take suka garzaya barikinsu suka dawo sanye da kayan sojoji dauke da bindigu kirar AK47, inda suka shiga harbin sama.

Daga cikin jama’an dake gargadin Sojojin akan su daina harbi akwai wata mata da aka fi sani da Mama Jude, watau mahaifiyar Jude, a nan aka fara cacar baki tsakanin Sojojin da wannan mata, ganin haka ya sanya mijinta wanda jami’in Dansanda ne mai mukamin Inspekta ya ture guda daga cikin Sojojin suka fara dambe.

Daga nan ne sai yaronsa Jude ya fara kuwwa yana gudu yana neman taimakon jama’a ga mahaifinsa, nan da nan wani Soja da ake yi ma lakabi da Buratai ya bindige yaron har sau uku a kirjinsa da hannunsa, anan take yaron ya fadi matacce.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

“Duk da cewa an garzaya da Jude zuwa Asibiti, bai kai da rai ba, amma mahaifinsa na samun kulawa a asibitin sakamakon yankan wuka da ya samu a wuya.” Inji wani da lamarin ya faru a gabansa, mai suna Bitrus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel