Mai hangen nesa: Yadda wani Malami ya gano Atiku zai yi nasara a 2019

Mai hangen nesa: Yadda wani Malami ya gano Atiku zai yi nasara a 2019

Tun kwanakin baya ne wani rikakken Malami yayi wani hasashe inda yace tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar zai yi nasara a zaben 2019 ko da kuwa babu kowa a gari.

Mai hangen nesa: Yadda wani Malami ya gano Atiku zai yi nasara a 2019
Wani rikakken Shehi ya gano cewa Atiku zai yi mulki a 2019
Asali: UGC

Limamin wani coci mai suna KKDM a cikin Jihar Ebonyi, Emmanuel Chukwudi ya taba fitowa ya bayyanawa Duniya cewa Atiku Abubakar ne zai lashe zaben 2019. Malamin ya bayyana wannan ne a wata hudubar sa a baya.

Wannan Bajimin Malami yayi wannan jawabi ne tun kwanakin baya a lokacin da babu wanda yake tunanin cewa Atiku zai kai labari. Dama dai a baya, babban Malamin na Kirista ya taba gano cewa Atiku zai tsere daga Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Tambuwal ya koma jaharsa don tsayawa takarar Gwamna

Yanzu dai wannan hangen da Malamin yayi game da Atiku na nema ya zama gaskiya inda tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya samu tikitin takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP. Atiku zai kara ne da Shugaba Buhari a zaben 2019.

Shehin Malamin dai ya gargadi manyan Sanatocin kasar irin su Bukola Saraki da Dino Melaye a wancan lokaci da cewa ana shirya masu makarkashiya a Jam’iyyar APC. Yanzu haka dai dukkan su sun tsere daga APC sun dawo PDP.

Dazu dai kun ji cewa Sanata Dino Melaye ya bayyana wanda zai lashe zaben 2019 tsakanin Atiku da Buhari inda yace Shugaban kasa Buhari zai tattara kayan sa ya koma Daura a shekara mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel