Jami’ar Karaduwa: Shahararren dan siyasa zai gina jami’a da kwalejin kimiyya a jahar Katsina

Jami’ar Karaduwa: Shahararren dan siyasa zai gina jami’a da kwalejin kimiyya a jahar Katsina

Daga karshe karancin manyan makarantun ilimi a yankin karaduwan jahar Katsina ya zo karshe a yayin da tsohon dan takarar gwamnan jahar Katsina Injiniya Nura Khalil ya dauki gabaran gina sabuwar jami’a da kuma kwalejin kimiyya da fasaha a yankin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin 8 ga watan Oktoba ne aka fitar da alamar makarantun biyu, da Nura Khalil zai gina a garin Funtuwa, watau Logo.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: Gwamna Tambuwal ya yi mubaya’a ga Atiku Abubakar

Da yake zantawa da majiyar tamu, Nura Khalili yace ba zai fasa gina wannan jami’a ba don kawai ya fadi zaben fitar da dan takarar Sanatan yankin Funtuwa na jam’iyyar APC ba, don haka yace zai cigaba da kokarin tabbatar da wannan jami’a.

Jami’ar Karaduwa: Shahararren dan siyasa zai gina jami’a da kwalejin kimiyya a Katsina
Jami’ar Karaduwa
Asali: Facebook

“Tabbas za’a gina wannan jami’a a garin Funtuwa don samar da ingantaccen ilimi ga matasanmu, babu gudu babu ja da baya game da samar da wannan makaranta, kuma za’a fara aikin ginnta nan gaba kadan.” Inji shi.

Ga duk mai bibiyan siyasan jahar Katsina ya san cewa jama’an yankin Karaduwa na kokawa bisa rashin wani babban makaranta a yankin nasu duk da cewa suna da dimbin al’umma, wanda har ta ga wasu na ganin tamkar makarkashiya ake musu.

Manyan makarantun dake jahar Katsina sun jada da jami’ar jahar Katsina ta tunawa da Umaru Musa Yar’adua, jami’ar gwamnatin tarayya, kwalejin ilimi na jaha, Kwalejin ilimi na gwamnatin tarayya da kuma kwalejin kimiyya da fasaha, kuma dukkaninsu na yankin Katsina ne, illa kwalejin ilimin dokoki dake garin Daura.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel