2019: Sharadi guda da Atiku zai cika idan yana son kuri'ar mu - 'Yan kabilar Igbo

2019: Sharadi guda da Atiku zai cika idan yana son kuri'ar mu - 'Yan kabilar Igbo

- Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta mika taron taya murnar ga Atiku Abubakar bisa lashe zaben cikin gida na PDP

- Sai dai kungiyar ta gargadi PDP cewar za ta goyi bayan wata jam'iyyar idan har Atiku bai zabo mataimakinsa daga cikin kabilar Ibo ba

- Kungiyar ta bayar da sunayen wasu shararun 'yan Najeriya da ta ganin za su dace ta takara tare da Atiku

Kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo reshen matasa ta mika sakon taya murnar ta ga dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar bisa nasarar da ya yi na lashe zaben fidda gwani da akayi ranar Lahadi a Port Harcourt.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya fafata da wasu 'yan takarar guda 11 amma shi ya zama zakara a karshen zaben.

Kara karanta wannan

Ba a tsame Atiku daga cikin yan takarar yarjejeniya ba, Saraki

KARANTA WANNAN: Dalilai 3 da ka iya sa Shugaba Buhari shan kasa a zaben 2019 dake tafe

Atiku Babban barawo ne a Afrika: Manyan badakaloli 5 da ya tafka - Rahoton Amurka
Atiku Babban barawo ne a Afrika: Manyan badakaloli 5 da ya tafka - Rahoton Amurka
Asali: Twitter

A jawabin da shugaban kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro ya yi bayan an kammala zaben, ya ce Atiku ne wanda ya cacanta da wannan aikin.

Sai dai kungiyar ta kuma ce muddin Atiku yana son ya yi nasara a babban zaben na 2019 sai ya zabo mataimakinsa daga yankin Kudu maso Gabas.

Kungiyar ta bayar da misalin 'yan takara kaman Peter Obi, Ngozi Okonjo Iwela, Sanata Dr Ike Ekweremadu da Sanata Enyinnaya Abaribe

Ya ce muddin ba'a zabi dan kabilar Igbo a matsayin mataimakin Atiku ba, ba za su zabi PDP a zaben shugabancin kasa ba domin yankin tana da mutanen da suka dace da wannan matsayin.

Kara karanta wannan

2023: An Siya Wa Bala Mohammed, Gwamnan Bauchi Fom Din Takarar Shugaban Kasa a PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel