Idan da ni barawo ne da tuni Buhari ya garkame ni a kurkuku - Atiku

Idan da ni barawo ne da tuni Buhari ya garkame ni a kurkuku - Atiku

- Dan takara shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya ce babu dan siyasar da aka bincika kamar sa a gwamnatin Buhari

- Atiku ya ce idan da an same shi da wata laifi ko satar kudin al'umma da tuni Buhari ya kulle shi

- Atiku ya kuma karyata zargin da kungiyar magoya bayan Buhari su kayi na cewar ya yi amfani da kudi wajen sayen kuri'u a zaben fidda gwani

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP ya ce idan da Shugaba Muhammadu Buhari yana da hujjar cewa ya saci kudin al'umma da tuni ya sa an kama shi.

A wata sanarwa da ta fito daga kungiyar yakin neman zabensa, Atiku ya ce nasarar da ya yi a zaben fidda gwani ya jefa magoya bayan Buhari cikin rudani.

Idan da ni barawo ne da tuni Buhari ya kama ni - Atiku
Idan da ni barawo ne da tuni Buhari ya kama ni - Atiku
Asali: Twitter

Ya kuma karyata zargin cewar ya yi amfani da kudi ne wajen zaben fidda gwani shiyasa ya yi nasara kamar yadda kungiyar yakin neman zaben Buhari ke ikirari.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 5 da Atiku ya fadi a jawabinsa na lashe zaben cikin gida na PDP

Atiku ya ce ya yi nasara ne bayan ya fafata da sauran masu neman takarar ba kamar Buhari da kawai jam'iyya ta mika masa tikitin takarar ba tare da wata hamayya ba.

"Ba muyi mamakin yadda magoya bayan Buhari suka kidime ba. Dama mun san cewar za su shiga rudanni saboda sun san cewar nasarar Atiku a PDP za ta kawo karshen mulkin su," inji shi.

Atiku ya ce har tsohon abokin takarar Buhari, Pastor Tunde Bakare ya yi hasashen cewar shine zai zama dan takarar jam'iyyar saboda shi dan takara ne wanda baya nuna banbanci tsakanin 'yan Najeriya.

"Duk 'yan Najeriya sun san cewar babu dan takarar da aka bincika kamar Atiku a karkashin mulkin Buhari, kuma da ace an same shi da wata laifi da tuni Buhari ya sa an daure shi saboda rashin yafiyarsa," inji Sanarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel