‘Dan Majalisan Sokoto ya rasa kujerar sa wajen wani Matashi
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Injiniya Aminu Isa wanda ke wakiltar Isa da Sabon Birni a Majalisar Wakilan Tarayya ya sha kunya inda ya rasa kujerar sa wajen wani Matashi mai shekaru 34.

Asali: Depositphotos
Honarabul Aminu Isa ya rasa tikitin Jam’iyyar APC na ‘Dan Majalisar Tarayya wajen wani Sabon-shiga Bello Shehu Suleiman. Bello Shehu dai Matashi ne wanda yake aiki Gwamnati kafin ya shiga harkar siyasa a halin yanzu.
Sulaiman mai shekaru 34 yana aiki ne a kamfanin NCS na Najeriya inda ya samu kuri’a 599 yayin da Abokin adawar ta sa Aminu Isa wanda ya samu kuri’a 591. Kuri’a 1 tak ne dai aka soke a zaben kamar yadda labari ya zo mana.
KU KARANTA: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Mark zai bar Majalisa bayan shekaru kusan 20
An dai dade ana dage zaben kafin a gudanar da shi wannan karo domin a gujewa fushin Hukumar zabe na kasa watau INEC. Aminu Isa wanda yake rike da kujerar a yanzu bai shigo wajen zaben na fitar da gwani da aka yi a Sokoto.
Dazu kun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki wadanda su ka sha kasa a zaben fitar da gwani a APC da su yi hakuri su cigaba da zama tare da Jam’iyyar domin APC ta tsira.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.
Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng