Abba Moro ya lashe kujerar Sanatan Benuwai ta Kudu a PDP

Abba Moro ya lashe kujerar Sanatan Benuwai ta Kudu a PDP

Mun samu labari cewa Sanata David B. Mark ya rasa kujerar sa ta Majalisar Dattawa a Jam’iyyar adawa ta PDP. Hakan na zuwa ne kuma bayan ya sha kashi a zaben takarar Shugaban kasa da ya shiga.

Abba Moro ya lashe kujerar Sanatan Benuwai ta Kudu a PDP
Mista Abba Moro zai nemi kujerar Benuwai ta Kudu a Majalisar Dattawa
Asali: UGC

Tsohon Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Mista Abba Moro ne ya samu tikitin Sanata na Mazabar Benuwai ta Kudu a Jam’iyyar PDP jiya. An gudanar da zaben ne har cikin dare a filin wasa na Aper Aku da ke Garin Makurdi.

Moro wanda yayi Minista a lokacin Jonathan ya samu kuri’a 461 ne a zaben inda wani tsohon ‘Dan Majalisar dokokin Jihar Hon Joseph Ojobo ya zo na biyu da kuri’a 365. Mike Onoja ne ya zo na uku da kuri’a 165 inji Malamin zaben.

KU KARANTA: 2019: Shugaba Buhari ya nemi ayi koyi da wani Gwamnan APC a Najeriya

Sunny Agbade ne ya sanar da sakamakon zaben wanda a baya an yi ta dage shi saboda wasu dalilai. David Mark ne dai wanda yake kan kujerar tun 1999. A wannan karo Sanatan ya nemi takarar Shugaban kasa inda ya sha kashi.

Abba Moro zai yi takara ne a zaben 2019 da wani tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Benuwa Steven Lawani a Jam’iyyar APC. A 2015 dai Mark wanda ya dade a kujerar ya gamu da barazana daga Daniel Onjeh na Jam’iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel