2019: Marawa Atiku baya, barin PDP da sauran abubuwan da Kwankwaso zai iya yi a siyasa

2019: Marawa Atiku baya, barin PDP da sauran abubuwan da Kwankwaso zai iya yi a siyasa

Kun samu labari cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP inda ya doke irin su tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Kwankwaso. Kwanaki ne dai Kwankwaso ya fice daga APC ya koma Jam’iyyar PDP.

2019: Marawa Atiku baya, barin PDP da sauran abubuwan da Kwankwaso zai iya yi a siyasa
Atiku ya doke su Kwankwaso wajen zaben fitar da gwani na PDP
Asali: UGC

Yanzu dai mun kawo maku manyan matakan da Kwankwaso zai iya dauka a Jam’iyyar PDP yayin da aka dunfari zaben 2019.

1. Takarar Sanata

Yanzu dai Rabiu Kwankwaso yana iya neman komawa Majalisar Dattawa inda yake wakiltar Kano ta tsakiya. PDP dai ta tsaida Hon. Aliyu Madakin Gini a matsayin wanda zai nemi kujerar Sanatan sai dai yana iya maye gurbin sa kafin zaben 2019.

KU KARANTA: Ka yafe mani: Kwankwaso ya ba Jonathan hakurin abin da ya faru a baya

2. Marawa Atiku baya

Haka kuma Sanata Rabiu Kwankwaso yana iya marawa Atiku Abubakar wanda ya samu tikitin PDP baya ya samu nasara a zaben 2019. Idan Atiku yayi nasara dai Kwankwaso na iya samun wani babban matsayi a cikin Gwamnatin sa.

3. Sauya-sheka

Abin da kuma ya ragewa Sanatan shi ne ya koma Jam’iyyar APC ko wata Jam’iyya bayan 2019 bayan an tika sa da kasa a 2019. Wasu dai su na ganin tuni tsohon Gwamnan na Kano ya lalata rawar sa da tsalle da ya bar Jam’iyyar APC.

Jiya ne ku ka ji cewa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma Mataimakin sa Namadi Sambo hakurin abubuwan da ya faru tsakanin su a 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel