Taron PDP: Dalilan da zasu sa wakilan jam'iyyar su zabi Tambuwal don ya kara da Buhari

Taron PDP: Dalilan da zasu sa wakilan jam'iyyar su zabi Tambuwal don ya kara da Buhari

- Dr Okey Ikechukeu, ya ce Gwamna Aminu Tambuwal ne kadai zai mulki Nigeria da tsarin shugabanci na karni na 21

- Gwamnan jihar Sokoto na daya daga cikin 'yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben fidda gwani da ke kan gudana

- Ikechuku ya jaddada cewa Tambuwal ya fi sauran yan takarar cancatar zama shugaban kasa, har da ma shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari

Kakakin kungiyar yakin zaben Tambuwal a matsayin shugaban kasa, Dr Okey Ikechukwu, ya ce Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ne kadai wanda zai iya shugabantar Nigeria irin salon mulkin karni na 21, wajen dawo da martar kasar a idon duniya.

Ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a ci gaba da babban taron jam'iyyar PDP da ke gudana a garin Fatakwal, jihar Rivers a yau Asabar, 6 ga watan Oktoba, inda wakilan jam'iyyar za su zabi dan takarar shugaban kasar da zai kara da Buhari na jam'iyyar APC.

Ya ce: "Tambuwal na da kwarewa da cancatar da ta zarce ta sauran yan takara karkashin PDP, kuma shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke takara a jam'iyyar APC.

Taron PDP: Dalilin da zai sa wakilan jam'iyyar su zabi Tambuwal don ya kara da Buhari
Taron PDP: Dalilin da zai sa wakilan jam'iyyar su zabi Tambuwal don ya kara da Buhari
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: Rundunar soji ta samu nasarar kashe mayakan Boko Haram 3 tare da cafke 1 a Borno

"Na daya, ya goge da sha'anin mulki kasancewar ya dade ana damawa da shi a harkar musamman a matakin kasa. Na biyu kuma, kowa ya sani cewa shi kwararre ne a fannin siyasa da kuma gina al'umma, wannan ya sanya muke kallonsa a matsayin shugaban da ya cancaci ya jagorance mu. Na uku, shi bai da wata matsala da fannin shari'ar kasar nan.

Na hudu, shine kadai dan takara a cikin sauran yan takarkarun da ya bayyana irin kyawawan manufofinsa da kuma bayyana hanyoyin da zai magance matsalolin da kasar ke fuskanta da zaran ya zama shugaban kasa," a cewar Ikechukwu.

Da aka tambaye shi kadan daga cikin kudurorin Tambuwal na sake fasalin kasar, Ikechukwu ya ce daga ciki akwai baiwa 'yan kasar zabin wadanda za su wakilce su a manyan hukumomi na kasar kamar su Hukumar da'a ta gwamnatin tarayya, hukumar iyakar kasa, da sauransu.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel