Wasikar El-Rufai ga Buhari: Zunubban Shehu Sani ga kai kanka shugaban kasa

Wasikar El-Rufai ga Buhari: Zunubban Shehu Sani ga kai kanka shugaban kasa

- An dade ba'a jituwa tsakanin Sanata Sani da Malam Rufai

- An gano wasika da wai aka ce Elruai ya rubuta wa shugaba Buhari

- A baya Elrufai ya tsine wa Shehu Sani

Wasikar El-Rufai ga Buhari: Zunubban Shehu Sani ga kai kanka shugaban kasa
Wasikar El-Rufai ga Buhari: Zunubban Shehu Sani ga kai kanka shugaban kasa
Asali: Twitter

A marga-margar siyasa dake wakana a Kaduna, bayan kulla-kullar da Sanata Shehu Sani yayi ta kawar da duk wata hamayya daga cikin gida a APC, gwamna El-Rufai bai ji dadin wannan ci gaba ba.

Majiyarmu ta bamu wata wasika da tace wai gwamnan ne ya rbuta wa shugaba Buhari don kawai ya lallai sai an hukumta Sanatan wanda basu ga maciji da juna.

Shima dai Uba Sani, hadimin Malamin gwamnan, ya garzaya kotu yace ai babu yadda za'a yi a ware shi a cikin jam'iyya duk da uban kudin da ya kashe na kamfe da takara.

DUBA WANNAN: Zamu daure duk mai hannu a rugujewar bankuna - Ministar Kudi

An gano wasu gwamnoni da suka je ganin shugaba Buhari a jiya, kan yadda suka ce Oshiomole Adams, na musu karfa-karfa a jihohinsu.

Ga abin da wasikar ta kumsa wanda bayan sallama ga shugaban, ta zayyana zunubai da wai Shehu Sani yayi ga shugaba Buhari a shekarun nan hu babu kadan:

1. Yace gwamnatinka akwai cin hanci da rashawa

2. Yace gwamnatin ka ce ta shirya sato matan Dapchi don siyasa

3. Yace murkushe IPOB cin zarafin bil Adama ne

4. Ya zolaye ka kan rashin lafiyarka da cewa ka fiye zuwa Ingila

5. A bana yace ka kasa kare kasar nan daga kashe-kashe

6. Yayi maka ba'a kan wai ka kula da gajere maii duka maka har kasa.

7. Yace kai ka haddasa rigimar cikin APC

8. Ina yi maka tuni da cewa kace in hukumtashi a jiha ta bayan rashin biyayya da yake nuna wa ga jam'iyya da ma gwamnati a sama da kasa.

Dawajewa; babu tabbaciin ko gwamnan ya rubuta hakan, sai munji daga bakinsa nan gaba.

:

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel