Zaben Fidda Gwani: Gwamna Yari zai kalubalanci shugaban jam'iyyar APC na kasa a jihar Zamfara

Zaben Fidda Gwani: Gwamna Yari zai kalubalanci shugaban jam'iyyar APC na kasa a jihar Zamfara

A jiya Juma'a gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Abubakara Yari, ya kirayi dukkanin magoya bayan sa akan su fito kwansu da kwarkwarta domin gudanar da zanga-zangar lumana dangane da hukuncin shugaban jam'iyyar APC na kasa kan zaben fidda gwani da aka gudanar a jiharsa.

Gwamna Yari ya yi wannan kirane domin magoya bayansa su bayyana rashin amincewarsu dangane da hukuncin shugabancin jam'iyyar APC da ta yi na soke zaben fidda gwanin takarar Gwamna da aka gudanar cikin jihar ta Zamfara a ranar Lahadin da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, Gwamna Yari ya nemi magoyan akan su fito cikin ayari zuwa babban ofishin hukumar 'yan sanda na jihar domin gudanar da zanga-zangar lumana da misalin karfe 10.00 na safiyar yau ta Asabar.

Gwamnan yayin ganawarsa da manema labarai cikin babban birnin jihar na Gusau ya bayyana cewa, wannan lamari na bayyana rashin amincewar su ba zai yanke ba har sai shugabancin jam'iyyar APC ta fahimci kuskurenta kan hukuncin da ta zartar.

Zaben Fidda Gwani: Gwamna Yari zai kalubalanci shugaban jam'iyyar APC na kasa a jihar Zamfara
Zaben Fidda Gwani: Gwamna Yari zai kalubalanci shugaban jam'iyyar APC na kasa a jihar Zamfara
Asali: UGC

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, Gwamna Yari na fafata wani bakin gumurzu tare da mutane 8 dake hankoron kujerar gwamnatin jihar dangane da yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin takara na jihar a makon da ya gabata.

KARANTA KUMA: Jami'ar Dakarun Soji ta yiwa Muhammad Indimi babban Karamci

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugabancin jam'iyyar APC na kasa baki daya ya soke zaben da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata inda ake sa ran sake gudanar da sabo a yau Asabar.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, jam'iyyar ta yi soke zaben ne sakamakon baranza gami da kwace da kuma fizgen akwatuna da kayayyakin zabe da wasu 'yan baranda suka aiwatar bisa ga 'yan siyasa da suka dauki nauyin wannan mummunan lamari.

Nan ba da jimawa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel