Rikicin APC: Bana son katsalandan – Oshiomole ga Gwamna Abdul Aziz Yari

Rikicin APC: Bana son katsalandan – Oshiomole ga Gwamna Abdul Aziz Yari

Uwar jam’iyyar APC ta kasa a karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar, Adams Aliyu Oshimole ta sana da rusa shuwagabannin jam’iyyar APC reshen jahar Zamfara sakamakon rashin bada hadin kai da suka yi wajen ganin an shirya sahihin zaben fitar da yan takarkarun jam’iyyar.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin APC, Yekini Nabena ne ya bayyana haka a ranar Juma’a 5 ga watan Oktoba a babban ofishin jam’iyyar dake babban birin tarayya Abuja, inda yace jam’iyya ta rushe duk wata tsagin APC dake Zamfara.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta jinginar da manyan tashohin sauka da tashin jiragen Najeriya

Nabena ya cigaba da cewa jam’iyyar za ta kafa kwamiti na musamman da za ta gudanar da zaben fitar da yan takarkaarun gwamna, Sanatoci, yan majalisun jaha da yan majalisun tarayya gaba daya a ranar Asabar 6 ga watan Oktoba.

Haka zalika uwar jam’iyyar ta gargadi gwamnan jahar Zamfara, Adul Azizi Yari da kada ya sake yayi ma kwamitin shishshigi akan aikin da uwar jam’iyyar APC ta daura mata, haka zalika ta ja kunnen rusassun shuwagabannin jam’iyyar da yi ma kwamitin katsalandan.

Idan za’a tuna hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, ta umarci dukkanin jam’iyyun siyasan kasar da su tabbata sun mika mata sunayen yan takarar da zasu wakilceta a zabukan shekarar 2019 zuwa ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoba.

A wani labarin kuma, jam’iyyar APC za ta gudanar da zabukan fitar da yan takarkarunta a jahar Kaduna, tun daga mukamin Sanata, majalsun tarayya da ma majalisun dokokin jahar biyo bayan rikita rikitan da jam’iyyar ta yi ta fama dasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel