Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya

Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya

A duk shekara, 'yan Najeriya su kan so su san wane gwamna ne yafi kwazo cikin gwamnoni jihohin kasar. Amsar wannan tambaya tana sauyawa daga shekara zuwa shekara.

A yau, mun kawo muku jerin gwamnoni 5 da suka yiwa takwarorinsu zara wajen ayyuka kamar yadda sakamakon zaben gwaji na yanan gizo ya bayyana a wannan shekarar.

Sai ku cigaba da karantawa domin ganin ko wane gwamnonin ne suke kan gaba a wannan shekarar.

Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Asali: UGC

Ga jerin gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu kwazo a shekarar 2018

5) Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa (Inganta rayuwar talakawa da cigaban matasa)

Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Asali: Depositphotos

An haifi Ifeanyi Okowa a ranar 8 ga watan Yulin 1959 a jihar Delta. Kafin shigarsa siyasa, Okowa ya kwashe shekaru yana aiki a matsayin likita kuma shine direktan Victory Medical Centre.

Tun bayan hawarsa mulki a 2015, Okowa ya rika samun yabo daga takwarorinsa gwamnoni da mutanen jihar Delta. Okowa ne aka zaba a matsayin gwamnan da yafi sauran samar da abubuwan gina al'umma. Ya fi mayar da hankali ne kan taimakawa matasa.

4) Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike (Ayyukan Gine-gine)

Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Asali: Depositphotos

An haife shi a ranar 13 ga watan Disamban 1967 a Rumuepirikom, Obio Akpor na jihar Rivers. Ya yi karatun digiri a fanin lauya da mulk da kuma siyasa. Ya yi kwashe shekaru yana aiki a matsayin lauya mai zaman kasnsa kafin ya shiga siyasa.

Ya zama gwamna a 2015 kuma a zaben jin ra'ayin al'umma na wannan shekarar, Wike ya lashe lambar yabo na gwamna mafi gwazo wajen ayyukan gine-gine.

3) Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai (Habbaka Ilimi)

Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Asali: Depositphotos

Nasir El-Rufai ya girma a jihar Kaduna amma an haife shi ne a ranar 16 ga watan Fabrairun 1960 a Daudawa da ke karamar hukumar Faskari na jihar Katsina. Ya na digiri a fannin nazarin Sufiyo (Quantity Survey) daga ABU Zaria kana ya yi digiri a karatun lauya da kuma digiri na biyu a fanin mulki.

El-Rufai ya zama gwamna a shekarar 2015 inda ya kaddamar da shirin bayar da ilimi kyauta daga Frimari har zuwa karamar Sakandare tare da kawo tsarin bawa dalibai abinci kyauta a makarantu wanda hakan yasa ya lashe lambar yabo na gwamnan da ya ciri tuta a fanin samar da ingantanccen Ilimi.

2) Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo (Zaman lafiya da Tsaro)

Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Asali: Depositphotos

An haifin Ibrahim Hassan Dankwambo a ranar 4 ga watan Afrilun 1962 Gombe. Kamar sauran gwamnonin da ke aka lissafo a baya, shima mutum ne da ya goge wajen karatun boko sosai. Yana da digiri daga jami'ar ABU, Jami'ar Legas da Jami'ar Igbenedion.

Kafin ya zama gwamna a 2011, ya yi aiki a babban bankin kasa CBN da Coopers & Lybrand. Ya kuma zama Akanta na jihar Gombe daga baya ya zama Akanta Janar kasa baki daya.

Dankwambo ne ya lashe lambar yabo na samar da tsaro da zaman lafiya a zaben jin ra'ayin.

1) Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode (Gwamnan da ya lashe zaben)

Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya
Asali: Facebook

An haife Akinwunmi Ambode a ranar 14 ga watan Yunin 1963 a jihar Legas. Yana da digiri a daga jami'ar Legas da kuma wasu shaidan karatun daga wasu jami'oin kasashen waje.

Ambode ya kashe shekaru 27 yana aiki da gwamnatin jihar Legas inda ya fara daga mataimakin ma'aji har zuwa Akanta Janar na Jihar.

A shekarar 2015, ya lashe zabe inda ya zama gwamna a jihar Legas inda ya kawo sauye-sauye masu amfani a bangarori daban-daban na jihar.

Sakamakon zaben jin ra'ayin ya nuna cewa Ambode ne ake ganin yafi dukkan sauran gwamnonin Najeriya kwazo da aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel