Ana zaton wuta a masaka: An daure wasu Sojoji shekara 5 akan laifin garkuwa da mutane

Ana zaton wuta a masaka: An daure wasu Sojoji shekara 5 akan laifin garkuwa da mutane

Kotun hukunta sojoji na rundunar Sojan kasa ta yanke ma wasu Sojoji guda biyu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar biyar sakamakon kamasu da tayi da laifin yin garkuwa da mutane, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Sojojin da aka yanke ma wannan hukunci akwai Sajan Aliyu Hassan da kofur Bello Nasiru, kamar yadda kaakakin rundunar Sojan kasa, Brigediya Texas Chukwu ya sanar, inda yace shugaban kotun, Birgediya Olusegun Adesina ne ya yanke wannan hukunci.

KU KARANTA: Wani Gwamna a Najeriya ya garkame gidan tsohon gwamnan jaharsa

A zaman shari’a da Adesina ya jagoranta daya gudana a barikin Sojoji na Maimalari, yace kotun ta kama Sojojin ne da laifin yin garkuwa da mutane da kuma kwatar kudi daga hannun jama’a, don haka ta yanke musu wannan hukunci tare da rage musu mukami zuwa igiya daya da mara igiya.

Ana zaton wuta a masaka: An daure wasu Sojoji shekara 5 akan laifin garkuwa da mutane
Sojoji
Asali: Twitter

Haka zalika kotun ta rage ma wasu Sojoji guda uku mukami bayan ta kamasu da laifin nuna ragonta, rashin da’a da kuma sakaci da aiki yadda ya kamata, Sojojin sun hada da kyaftin Alhamdu Kwasau, Kyaftin Jimen Babangida da Laftanar Sunusi Bello.

Kotun ta kama Kwasau da laifin ragonta da sakaci da aiki don haka ta rage masa mukami zuwa laftanar tare da dauke masa izinin bada umarni na tsawon shekaru biyu, shima Kyaftin Babangida an dauke masa izinin bada umarni na tsawon watanni tara, kamar yadda shima Bello ya samu na watanni shida.

Daga karshe shugaban Kotun Adesina yace an kafa kotun ne domin ta tabbatar da dakarun Sojojin na bin dokokin aiki a yayin yaki da ta’addanci sau da kafa, tare da tabbatar dsa yancin dan adam a yayin aikin nasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel