Masu daukar hoton selfie a wuraren ganganci 259 ne suka mutu a shekaru shida
- Matasa na son daukar hoto don yadawa a kafafen sada zumunta
- A wasu lokutan sukan yi ganganci don birgewa
- An yi kira ga gwamnatoci su kiyaye

Asali: Getty Images
Samari da'yan mata, a zamanin yanar gizo da soshiyal midiya, sun duqufa wajen ganin sun yi kyau a hoto sannan su yada shi ga abokai.
A wani bincike da aka yi a fadin duniya, na National Library of Medicine wanda ke Amurka, an gano a tsakanin 2011 zuwa 2017, akalla mutum 260 ne suka mutu garin kokarin daukar hoto a wurare masu 'qayatarwa'.
Binciken, ya nuna yadda ake fakewa da gayu ake burmawa ga halaka, duk don neman suna da ganganci.
DUBA WANNAN: Abubuwa 10 da Kwankwaso zai iya koya daga Tinubu
Kungiyar likitoci, ta Amurkar, tace ya kamata ne ayi dokoki da zasu hana samari da 'yan mata gigin ganganci.
Kasashen da aka fi samun mutuwar dai, a binciken, sun hada da India, Rasha, US/Amurka, sai Pakistan, kuma mata ne suka fi mutuwa a gangancin.
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng