Cikin Hotuna: Wata Mata ta Haifi 'Yan 3 duka Maza a jihar Kano

Cikin Hotuna: Wata Mata ta Haifi 'Yan 3 duka Maza a jihar Kano

A can jihar Kano ne dake Arewacin Najeriya muka samu rahoton wata Mata mai matsakaitan shekaru, Dausiyya Kabiru Ibrahim, da ta haifi santala-santalan jarirai uku duka maza gwanin sha'awa da tuni an rangada ma su suna a jiya Alhamis.

A yayin ganawar mu da Mahaifin wannan Jarirai, Aramma Kabiru Ibrahim, ya shaida mana cewa an haifin jariran ne a wani karamin Asibitin kudi na Jega Clinic and Maternity da halin yanzu ya rada ma su sunayen Muhammad, Mahmud da kuma Hussaini.

Legit.ng ta fahimci cewa, Dausiyya ta haife jariranta Asibitin na Jega sakamakon rashin amsar su a Asibitin Murtala Muhammad dake birnin Jihar a sanadiyar yajin aikin kungiyar kwadago da ya wakana a makon da ya gabata.

Aramma Kabiru wanda mazaunin Unguwar Sheka Aci Lafiya dake karkashin karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, ya bayyana mana farin cikinsa kwarai da aniyya tare da mika godiyarsa ga Mahallaci dangane da wannan baiwa da kuma tabbaraki.

Cikin Hotuna: Wata Mata ta Haifi 'Yan 3 duka Maza a jihar Kano
Cikin Hotuna: Wata Mata ta Haifi 'Yan 3 duka Maza a jihar Kano
Asali: UGC

Asali: Original

Sai dai ko shakka ba bu yanayi na halin rayuwa a sanadiyar binciken da muka gudanar ya tabbatar mana da cewa, Aramma Kabiru ya na da bukatar agajin duk wasu masu hali da kuma ke da wadatar zuciya mai kyautatawa da za su tallafa masa wajen daiwainiyya da 'ya'yan sa.

KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta gurfanar da Hadimin Saraki kan Zambar N3.5b

A yayin yunkurin rufe asirin su Mahaifiyar wannan jarirai, Dausiyya, ta bayyana cewa Mijinta yana da matukar kwazo wajen sauke nauyin iyalansa da ya rataya a wuyansa ta hanyar sana'arsa ta dinkin hannu.

Sai dai yayin da Hausawa kan ce ido ba mudu ba ya san kima, jaridar Legit.ng ta fahimci cewa akwai bukatar masu hali su kai tallafi ga wannan Magidanci inda muka kawo mu ku lambar wayarsa kamar haka: 08063429210.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel