An kashe mutum daya tare da raunata wasu 10 a wurin zaben fidda ‘yan takara na APC

An kashe mutum daya tare da raunata wasu 10 a wurin zaben fidda ‘yan takara na APC

An kashe mutum daya tare da raunata wasu 10 bayan wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari wurin zaben fitar da ‘yan takarar kujerun majalisar jiha da tarayya da aka gudanar a Epe dake Legas, yau, Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewar mutumin da aka kashe sunansa Idris Alooma, kuma yana da shekaru 30 na haihuwa.

Rikici ya barke ne bayan an gama tantance daliget sun shiga wurin taron gudanar da zabukan sun kada kuri’ansu amma sai jagororin gudanar da zaben suka fara kidayar kuri’un bisa son ransu, ba yadda daliget suka gudanar da zaben ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar tun daliget na kan layi domin kada kuri’a da misalign karfe 3:45 na rana, jami’an zaben suka fara sanar da sakamako.

An kashe mutum daya tare da raunata wasu 10 a wurin zaben fidda ‘yan takara na APC
Wani wurin zaben fidda ‘yan takara na APC
Asali: Facebook

Wasu daga cikin mazabu da aka gudanar da zaben sun hada da Ibonwon, Ikosi-ejirin, Ogunmodede da sauran su.

Wani shaidar ganni da ido, Akeem Lawal, ya bayyana cewar an kasha Alooma ne da misalign karfe 4:15 na yamma bayan an kamala zabe, ana zaune domin jiran sakamako.

“Wanda ya jagoranci ‘yan dabar da suka kashe Alooma sunansa Wale Sabano,” a cewar Lawal.

DUBA WANNAN: Rikici ya barke a PDP a Kano bayan Kwankwaso ya yi zaben dan takara a gidansa

Wakilin NAN day a halarci wurin zaben ya bayyana cewar fusatattun matasa sun cinnawa motoci da gidajen jama’a wuta.

Adeyeri Sunday, jami’in dan sanda na a ofishin Epe, ya shaidawa NAN cewar sun yi nasarar kama daya daga cikin ‘yan dabar tare da bayyana cewar zasu yi kokarin ganin ragoqwar ma sun shigo hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel